Jerin Sunayen Ministocin Tinubu Da Ke Amsar Kudin Fansho Daga Jihohinsu

Jerin Sunayen Ministocin Tinubu Da Ke Amsar Kudin Fansho Daga Jihohinsu

An rahoto cewa har yanzu wasu daga cikin ministocin Shugaba Tinubu na cigaba da karɓar kuɗaɗen fansho daga jihohinsu.

Waɗannan ministocin dai tsofaffin gwamnoni ne a jihohinsu sannan har yanzu suna karɓar kuɗin fansho daga asusun jihohinsu.

Ministocin Tinubu masu karbar fansho a jihohinsu
Ministocin dai sun kasance tsofaffin gwamnoni ne a jihohinsu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ministocin da har yanzu su ke karɓar kuɗin fansho sun haɗa da:

Nyesom Wike

Wike an ba shi muƙamin ministan birnin tarayya Abuja, sannan ya riƙe kujerar gwamnan jihar Rivers har sau biyu a jere.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yin gwamnan da ya yi sau biyu a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sanya yana da damar a riƙa biyansa fansho.

Abubakar Badaru

Badaru ya yi gwamnan jihar Jigawa har sau biyu a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), hakan ya sanya ya cancanci samun kuɗin fansho daga asusun jihar.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Tsohon gwamnan shi ne wanda aka ba muƙamin ministan tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu.

Bello Matawalle

Matawale an ba shi muƙamin ƙaramin ministan tsaro a gwamnatin Shugaba Tinubu, muƙamin da mutane da dama suka yi ta maganganu a kansa.

Matawalle yana daga cikin ministocin Tinubu da su ke amsar kuɗin fansho daga jihohinsu, saboda ya yi gwamnan jihar Zamfara sau ɗaya.

Adegboyega Oyetola

Kamar Matawalle, Oyetola ya yi gwamnan jihar Osun sau ɗaya kuma yanzu haka yana daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar masu karɓar kuɗin fansho daga asusun jihar.

Bayan ya yi rashin nasara wajen yin tazarce, Shugaba Tinubu ya naɗa shi muƙamin ministan sadarwa, inda za a rantsar da shi a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

David Umahi

Sabon ministan ayyukan ya yi gwamnan jihar Ebonyi har sau biyu inda yake karɓar kuɗin fansho daga jihar ta yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sake Aikewa Da Sabon Gargadi Ga Sojojin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar

Ya yi shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sannan ya yi takarar neman tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Sauran ministocin masu karɓar fanshon daga jihohinsu

Sauran ministocin Shugaba Tinubu waɗanɗa ake zargi da karɓar fanshi daha jihohinsu, sun haɗa da

1. Simon Lalong (Jihar Plateau)

2. Atiku Bagudu (Jihar Kebbi)

3. Ibrahim Geidam (Jihar Yobe)

Tinubu Zai Rantsar Da Ministoci Ranar Litinin

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da ministocin da ya naɗa a ranar Litinin 21 ga watan Agusta.

Shugaban ƙasar zai rantsar da ministocin ne bayan majalisar dattawa ta tantancesu tare da amincewa da naɗin da ya yi musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng