Wasu 'Yan Arewa Ba Su Hakura ba, Sun Bukaci Tinubu Ya Ajiyewa El-Rufai Kujerar Ministan Kaduna
- Wata kungiyar arewa ta bayyana rashin tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin makarkashiya
- Kungiyar mai suna 'Like Minds Forum of Nigeria' ta nanata cewa ci gaban wani yunkuri ne da wasu ke yi don daukar fansa a kan El-Rufai
- An bukaci majalisar da ta wanke sannan ta tabbatar da tsohon gwamnan domin shawo kan tashin hankalin da ke kewaye da nadinsa
Jihar Kaduna - Wata kungiya mai suna 'Like Minds Forum of Nigeria', ta soki takkadamar da ke kewaye da nadin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da aka yi a matsayin minista.
Kungiyar ta arewa ta soki majalisar dattawan Najeriya kan kin tabbatar da El-Rufai a matsayin minista, inda ta bayyana hakan a matsayin kuskure da tabarbarewar siyasa.
Kungiyar arewa ta bukaci kujerar minista da aka kebewa El-Rufai
Kungiyar, ciki harda wasu da suka riki mukaman siyasa a gwamnatin El-Rufai, sun lura cewa tsarin tabbatar da El-Rufai a matsayin minista bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya zabe shi ya dauki sabon salo saboda makarkashiya da wasu ke yi wa tsohon gwamnan, Channels TV ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kaduna a ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, jagoran kungiyar kuma tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Shehu Muhammad, ya yi kira ga majalisar dattawa da ta gaggauta tantancewa da tabbatar da El-rufai kamar yadda ta yi wa sauran zababbun ministoci.
Ya ce akwai bukatar aikata hakan domin shawo kan tashin hankali da rudanin da ake ciki a arewa da sauran yankunan kasar.
Hadimin Buhari ya bayyana inda El-Rufai yake
A gefe guda, mun ji a baya cewa Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ke ƴan kwanaki kaɗan bayan majalisar dattawa ta ƙi amincewa ya zama minista.
Ahmad, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter @BashirAhmaad, a ranar Talata, 15 ga watan Agusta, ya sanya hoton Nasir El-Rufai.
Tsohon hadimin na Buhari ya yi wani rubutu mai cewa "Shaƙatawa a Dubai" a yayin wallafa hoton da ya yi. Birnin Beirut shi ne birni mafi girma a Lebanon kuma shi ne babban birnin ƙasar.
Asali: Legit.ng