Nyesom Wike: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Gameda Ministan Tinubu Na Birnin Tarayya

Nyesom Wike: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Gameda Ministan Tinubu Na Birnin Tarayya

  • Sanar na sunan Wike a matsayin ministan birnin Tarayya a gwamnatin Bola Tinubu ya bai wa al'umma da dama mamaki
  • Sai dai gabanin wannan nadin da aka yi ma sa, ya rike mukamai da dama a can baya
  • Legit.ng a cikin wannan maƙala ta zaƙulo wasu muhimman abubuwa dangane da Wike da jama'a da dama ba su sani ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Nyesom Wike sunane da ya karaɗe ko ina a cikin siyasar Najeriya har ma da wasu wuraren a ƙasashen waje.

Wike ya yi aiki tuƙuru wajen kawo ci gaba a jiharsa wato jihar Ribas, da ma yankinsa baki daya a lokacin da yake kan kujerar gwamna.

Bola Tinubu ya sanar da naɗin Nysome Wike a matsayin ministan Birnin Tarayya (FCT), Abuja a ranar Laraba da ta gabata.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi Ya Tona Masu Karkatar da Shugaba Tinubu da Muguwar Shawara

Abubuwan da ya kamata ku sani gameda Wike
Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba gameda Wike. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin wannan maƙala, Legit.ng ta tattaro muku muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani gameda Nysome Wike.

1. Kasancewar Wike lauya

Wike masanin shari'a ne mai lasisi da ya yi aikin lauya a shekarun baya, wanda a nan ne wasu suke ganin ya samo rashin tsoronsa da jajircewar da yake da ita.

Wike ya yi karatun digirinsa a ɓangaren shari'a a jami'ar Patakwal, wanda bayan nan ya yi aiki a babbar kotun tarayya.

Haka nan kuma matar Nysome Wike mai suna Eberechi, mai shari'a ce a babbar kotun jihar Ribas.

2. Wike ya riƙe minista lokacin Jonathan, COS lokacin Amaechi

Wike ya riƙe muƙamin ƙarami da babban ministan ilimi a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP

Haka nan Wike ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukuma a jihar Ribas, kafin daga bisani ya riƙe muƙamin shugaban ma'aikata (COS), a gwamnatin Rotimi Amaechi na jihar ta Ribas.

3. Kujerar gwamnan jihar Ribas

Nyesom Wike ya shugabanci jihar Ribas a matsayin gwamna daga shekarar 2015 zuwa 2023.

A lokacin da yake gwamna, ya mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi gine-gine, gyaran hanyoyi da inganta kiwon lafiya a jihar.

4. Akidar siyasa

Nyesom Wike ya kasance mai zazzafar aƙidar siyasa, kuma yana tsayawa tsayin daka kan duk wani abu da ya shafi yankin Neja-Delta.

Wike na yawan samun saɓanin ra'ayi da jama'a da dama, wanda hakan ke sanyawa ya janyo cece-kuce a al'amuran Najeriya da dama.

5. Nasarorin da ya samu a rayuwa

Nysome Wike ya samu lambobin girmamawa da dama bisa ga irin ƙoƙarin da ya yi wajen ciyar da jihar Ribas gaba kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Jajircewarsa wajen samar da ingantaccen yanayi a Ribas, ya bai wa jihar damar samun haɓakar harkokin kasuwanci a jihar.

Nysome Wike ya ziyarci Ganduje

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ziyarar da tsohon gwamnan jihar Ribas, Nysome Wike ya kai wa tsohon gwamnan Kano, kuma shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Ganduje.

An bayyana cewa Wike ya ziyarci Ganduje ne domin ya taya shi murnar zama sabon shugaban jam'iyyar APC da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng