Gwamnan Jihar Rivers Ya Shiga Karar Gwamnoni Da Buhari Kan Naira A Kotun Koli

Gwamnan Jihar Rivers Ya Shiga Karar Gwamnoni Da Buhari Kan Naira A Kotun Koli

  • An shiga zaman gwamnonin Najeriya guda 11 da gwamnatin tarayyya kan lamarin sauya fasalin Naira
  • Gwamnan jihar Rivers ya cika alkawarinsa na shiga cikin kara da wasu takwarorinsa suka riga suka yi
  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da Yahaya Bello na Kogi ne ke jagorantar wannan gwagwarmaya

Abuja - Gwamnatin jihar Rivers ta shiga karar da gwamnatocin jiha goma (10) suka shigar kan gwamnatin tarayya game da lamarin sauya fasalin Naira.

Karar da gwamnatin jihar Kaduna, Kogi, da Zamfara suka fara shigarwa a makonnin baya na kira ga kotun koli ta dakatar da gwamnatin tarayya wajen tilasta daina amfani da tsaffin takardun kudi N200, N500 da N1000.

A ranar 8 ga Febrairu kotun koli ta dakatar da CBN daga hana amfani da tsaffin Naira kafin ta yanke hukunci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Kotu Ta Amincewa Gwamnati Kwace Wasu Kadarori 14 Da Ake Zargin na Gwamnan Kogi ne

Tun daga lokacin sauran jihohi bakwai suka shiga lamarin suna masu goyon bayan takwarorinsu.

Sun hada da Ondo, Ekiti, Katsina, Ogun, Cross River, Lagos, da Sokoto

Amma jihohin Bayelsa da Edo kuwa, sun shiga matsayin masu goyon bayan gwamnatin tarayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotunkoli
Karar Gwamnoni Da Buhari Kan Naira A Kotun Koli
Asali: Facebook

A zaman dake gudana a kotu yanzu haka yau Laraba, Lauyan jihar RIvers, Emmanuel Ukala, ya shigar da jihar cikin lamarin matsayin mai goyon bayan sauran gwamnoni 10, rahoton TheCable.

Alkalan kotun guda bakwai sun amince da wannan bukatar.

Har yanzu ana zama a kotun don sauraron yadda zata kaya.

Ku kasance tare da Legit Hausa don samun bayanai kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel