Cire Tallafi: Tinubu Ya Bai Wa 'Yan Najeriya Haƙuri, Ya Ce Za a Dara Nan Gaba
- Shugaba Bola Tinubu ya roƙi 'yan Najeriya da su ƙara haƙuri kan halin da ake ciki
- Ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su yi dariya a gaba idan suka jure wahalhalun da suke sha a yanzu
- Ya tabbatar da ba da umarnin raba kayayyakin tallafi a duka jihohin Najeriya domin ragewa al'umma raɗaɗin rayuwa
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci 'yan Najeriya da su ƙara haƙuri da tsare-tsaren gwamnatinsa da 'yan Najeriya ke shan wahala saboda su.
Ya ce wahalhalun da ake sha a yanzu saboda cire tallafin man fetur, za su bude hanyoyin jin daɗi a gaba.
Ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani littafi na tarihin rayuwar babban mai faɗa a ji Edwin Clark kamar yadda The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ba da haƙuri, ya sanar da rabon kayan tallafi
Da yake jawabi a wajen taron ta hannun sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, Tinubu ya bayyana cewa yanzu haka ya ba da umarnin raba kayayyakin tallafi domin ragewa al'umma raɗaɗi.
Ya ce yanzu haka sun ba da umarnin fitar da manyan motoci 100 na kayayyakin tallafi, da 100 na kayayyakin abinci da kuma na takin noman zamani domin ragewa jama'a raɗaɗin rayuwar da cire tallafin mai ya jefa su.
Ya ƙara da akwai ƙarin waɗansu kayayyakin tallafin da za su biyo baya, inda ya buƙaci 'yan ƙasa da su ƙara haƙuri wajen ganin an gina gobe mai kyau kamar yadda The Sun ta wallafa.
Akume ya yabawa Tinubu kan naɗe-naɗen ministoci
George Akume ya kuma yabawa Tinubu kan yadda ya raba muƙamai ga ministocinsa da aka sanar a makon da muke ciki.
Ya ba da misali da sanar da Dave Umahi a matsayin ministan ayyuka da Tinubu ya yi, da cewa abu ne da ke nuni da cewa shugaban yana ba da muƙamansa ne bisa ƙoƙarin da mutum ya yi a muƙaman da ya riƙe a baya.
Ya bayyana cewa Dave Umahi ya yi aiki tuƙuru ga mutanensa a lokacin da yake gwamna, inda ya bayyana cewa Tinubu ya ɗauko hanyar da ta dace wajen tafiyar da gwamnatinsa.
Tinubu ya yi ƙarin haske dangane da batun maido da tallafin mai
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da Fadar shugaban ƙasa ta yi dangane da batun da ake yaɗawa, na cewa za ta maido da tallafin man fetur.
Fadar shugaban ƙasan ta musanta jita-jitar, inda ta tabbatar da cewa tallafin man da aka cire ya tafi, ba za a sake maido da shi ba.
Asali: Legit.ng