Cire Tallafin Man Fetur: Kwamitin Rabon Kayan Tallafi na Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Sabbin Bayanai

Cire Tallafin Man Fetur: Kwamitin Rabon Kayan Tallafi na Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Sabbin Bayanai

  • An tababtarwa da ƴan Najeriya cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haifar
  • Shugaban kwamitin rabon kayan tallafin, gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su dara nan bada jimawa ba
  • Nasir, gwamnan jihar Kebbi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli a lokacin taron kwamitin a birnin tarayya Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja- Kwamitin rabon kayan tallafi kan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya kafa, ya gudanar da taro a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli a birnin tarayya Abuja.

A cewar rahoton Premium Times, gwamnonin Bauchi, Bala Mohammed, Charles Soludo na jihar Anambra, Uba Sani na jihar Kaduna da Hyacinth Alia na jihar Benue, da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu, Ya Gayawa 'Yan Najeriya Muhimmin Abu 1 Da Za Su Yi

Kwamitin rabon kayan tallafi ya fitar da sabbin bayanai
Kwamitin ya ce nan bada dadewa ba 'yan Najeriya za su dara Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin rabon kayan tallafin, gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya bayyana cewa ana ci gaba da shirye-shirye domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin ga ƴan Najeriya.

Gwaman wanda ya bayyana hakan ta hannun wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ahmed Idris, ya fitar, ya ƙara da cewa nan bada daɗewa ba ƴan Najeriya za su dara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin ya bayar da tabbacin za a ci gajiyar ayyukansa nan bada daɗewa ba

Gwamnan ya bayyana cewa kwamitin yana yin iya bakin ƙoƙarinsa domin rage raɗaɗin halin matsin da ake ciki.

A kalamansa:

"Kwamitin ya zauna inda ya tattauna kan hanyoyin da za a rage raɗaɗin cire tallafin man fetur sannan nan bada jimawa ba ƴan Najeriya za su fara cin gajiyar hakan."
"A shirye mu ke mu samar da hanyoyi masu kyau waɗanda za su amfani ƴan Najeriya, don haka ku kwantar da hankalinku, kwamitin a shirye yake ya sauke nauyin da ke kansa."

Kara karanta wannan

Badakalar N1bn: Kotu Ta Bayar Da Sabon Umarni a Shari'ar Tsohon Kwamishinan Ganduje

"Abinda mu ke buƙata kawai shi ne haƙuri, goyon baya da haɗin kai daga wajen ƴan Najeriya domin mu samu damar cimma kuɗirori da manufofin kafa wannan kwamitin wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi."

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi magana kan tallafin N8,000 da Shugaba Tinubu zai rabawa iyalai 12m a Najeriya

Obi ya bayyana cewa tallafin ya yi kaɗan duba da yadda mutane suka tsinci kansu a cikin halin ƙaƙanikayi a dalilin cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng