Jerin Ma'aikatu 10 Masu Muhimmanci a Gwamnatin Tinubu, Da Ministocin Da Za Su Jagorancesu
A ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, Shugaba Tinubu ya rabawa ministoci 45 da ya naɗa, muƙaman da za su riƙe.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Sai dai, 10 daga cikin ma'aikatun ana yi musu kallon masu matuƙar muhimmanci ga ƴan Najeriya da nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu.
Muhimman ministoci 10 da ma'aikatunsu
A cewar @StatiSense, waɗannan ma'aikatun da ministocin na gwamnatin Tinubu, na da matuƙar muhimmanci:
- Albarkatun man fetur: Shugaba Bola Ahmed Tinubu – Jihar Legas
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda yake a gwamnatin da ta gabata, shugaban ƙasa Bola Tinubu, shi ne jagoranci ma'aikatar albarkatun man fetur.
- Kudi da tattalin arziƙi: Wale Edun – Jihar Ogun
Wale Edun shi ne ministan kuɗi da tattalin arziƙi.
- Ayyuka : David Umahi – Jihar Ebonyi
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, wanda ya yi ƙoƙari sosai a ɓangaren ayyukan raya ƙasa, zai jagoranci ma'aikatar ayyuka.
- Makamashi: Adebayo Adelabu – Jihar Oyo
Adebayo wanda tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ne, zai jagoranci ma'aikatar makamashi.
- Ilmi: Tahir Mamman - Jihar Adamawa
Mamman shi ne shugaban jami'ar Baze, da ke Abuja. Tahir, Farfesa ne a ɓangaren shari'a kuma tsohon Darekta Janar na makarantar lauyoyi ta ƙasa.
- Lafiya: Ali Pate - Jihar Bauchi
Ali Pate ya riƙe muƙamin ƙaramin ministan lafiya a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, daga shekarar 2011 zuwa 2013.
- Tsaro: Mohammed Badaru – Jihar Jigawa
Mohammed Badaru shine tsohon gwamnan jihar Jigawa.
- Cikin gida: Sa'idu Alkali – Jihar Gombe
Alkali sanata ne wanda ya wakilci Gombe ta Arewa har sau uku.
- Sadarwa da tattalin arziƙin zamani: Bosun Tijani – Jihar Ogun
Bosun Tijani wanda ƙwararre ne a ɓangaren fasahar sadarwa, ɗan kasuwa kuma mai zuba jari, zai jagoranci ma'aikatar sadarwa.
- Harkokin gona da abinci: Abubakar Kyari - Jihar Borno
Tsohon sanata mai wakiltar Borno ta Arewa a majalisar dattawa ta tara, zai jagoranci ma'aikatar harkokin gona.
Ministocin Birnin Tarayya Abuja
A baya rahoto ya zo kan ministocin da suka taɓa riƙe muƙamin ministan babban birnin tarayya Abuja.
Tsohon gwamna Wike, shi ne sabon ministan birnin tarayya Abuja. Kafin zuwan Wike akwai ministoci 7 da birnin tarayya Abuja, ya yi tun daga shekarar 1999.
Asali: Legit.ng