Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13

Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya rabawa ministocinsa ayyukan da za su yi, kimanin mako guda bayan majalisar dattawan Najeriya ta tantance su
  • Ofishin shugaban kasa ne ya sanar da mukaman ministocin wanda ake ta zuba idon gani a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu
  • Sabanin adawar da wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya nuna, shugaban kasar ya ci gaba da rike mukaman kananan ministoci

Abuja - Bayan rabawa ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu mukamai da aka yi a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, ya nuna cewa shugaban Najeriyan ya yi watsi da tangardar da Festus Keyamo ya gano.

Keyamo, babban lauyan Najeriya (SAN), ya kasance karamin ministan kwadago da daukar ma'aikata a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

El-Rufai, Abba Gana: Cikakkun Sunayen Ministocin Babban Birnin Tarayya Tun 1999

A ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, Shugaban kasa Tinubu ya nada Keyamo mai shekaru 53 a matsayin sabon ministan sufurin jiragen sama na kasar.

Shugaban kasa Tinubu ya nada kananan ministoci duk da shawarar da Keyamo ya ba shi
Mukaman Ministoci: Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Watsi Da Keyamo, Ya Nada Kananan Ministoci 13 Hoto: Festus Keyamo, ESQ, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban kasa Tinubu ya yi watsi da korafin Keyamo

Legit.ng ta tuna cewa yan kwanaki kafin cikar wa'adin gwamnatin da ta gabata - a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu, 2023 - Keyamo, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar nada ministoci don su ci gashin kansu, cewa mukamin karamin minista ya saba kundin tsarin mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shawarar tasa na kunshe ne a cikin jawabin bankwana da ya yi a zauren majalisar fadar shugaban kasa, rahoton The Punch.

Dan siyasar wanda ya kasance haifaffen dan jihar Delta ya yi muhawara cewa mukamin 'karamin minista' baya aiki a bangaren mutane da dama da aka nada a kujerar.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Lokacin Da Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa

Ya bayyana cewa zai yi wahala a tantance ayyukan kananan ministoci tunda an yi ma aikinsu kaca-kaca a karkashin na ministoci.

A cewarsa, duk wasu shawarwari da karamin minista zai kawo sai wani abokin aikinsa ya tantance kafin ya iya isa majalisa don amfani da shi, rahoton Vanguard.

Sai dai kuma, Shugaban kasa Tinubu bai kula da martanin Keyamo ba sannan ya ambaci sunayen kananan ministoci 13.

Sune:

  1. Bello Matawalle - Karamin Ministan tsaro
  2. Abdullahi Gwarzo - Karamin ministan gidaje da raya birane
  3. Yusuf T. Sunumu – Karamin Ministan ilmi
  4. Mariya Mahmud – Karamar Ministan Abuja
  5. Bello Goronyo - Karamin Ministan ruwa
  6. Maigari Ahmadu – Karamin Ministan karafa
  7. Aliyu Sabi Abdullah – Karamin Ministan gona da abinci
  8. Ishak Salako – Karamin Ministan muhalli
  9. Heineken Lokpobiri – Karamin Ministan man fetur
  10. Tunji Alausa – Karamin Ministan lafiya da kula da jama’a
  11. Nkiruka Onyejeocha – Karamar Ministan kwadago da samar da ayyuka
  12. Ekperikpe Ekpo – Karamar Ministar gas
  13. Imman Suleiman Ibrahim – Karamar Ministar harkokin ‘yan sanda

Kara karanta wannan

“Bai Kamata Ya Zama Na Siyasa Kawai Ba”: Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Nada Matawalle Ministan Tsaro

Fadar shugaban kasa ta fadi lokacin da Tinubu zai rantsar da ministoci

A gefe guda, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, a cibiyar taro na fadar shugaban kasa, Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.

Babban sakatern gwamnatin tarayya, Dr George Akume, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng