Zunubai 10 Da DSS Suka yi Amfani Da Shi a Kan El-Rufai Wajen Tantance Ministoci
- Wasu abubuwa da-dama su ka hana Nasir El-Rufai a amincewa Nasir El-Rufai ya zama Minista
- Ana zargin DSS ta fake da irin kalamai da ayyukan ‘dan siyasar wanda za su iya raba kan jama’a
- Sannan ana tuhumar gwamnatin El-Rufai da jefa al’umma a kangi a sanadiyyar tsare-tsarensa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Zargi dabam-dabam da su ka hada da sakin baki da tulin korafi su ka kawowa Malam Nasir El-Rufai tasgaro wajen zama ministan tarayya.
A rahoton Premium Times, an tattaro jerin zargin da ake yi wa tsohon Gwamnan, hakan ya jawo aka gaza amince masa da ya rike mukami a gwamnati.
Daga zargin korafi zuwa tauye akkin jama’a, majiya daga hukumar tsaro ta DSS ta bayyana zargin da ake yi wa El-Rufai, sai dai ba mu tabbatar da su ba.
1. El-Rufai bai tsoron sakin maganganu
Rahoton ya ce daga cikin manyan zargin da ake yi wa Malam El-Rufai shi ne ya na yin maganganun da ke iya jawo rikici tsakanin al’ummar Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A bayan nan, an ji shi ya na fadawa malaman addini dalilin da ya sa jam’iyyarsa ta APC ta ke tsaida musulmi da musulmi takarar Gwamna a Kaduna.
2. Cin zarafin Bil Adama
Daga zargin da ake yi masa akwai cin zarafi da hakkin al’umma, daga ciki akwai zarginsa da hannu wajen hallaka Ibraheem El-Zakzaky da mabiyansa.
Rikicin Gwamnatin Kaduna da El-Zakzaky ya kai gaban kotun ICC da majalisar dinkin Duniya.
3. Zargin facaka da dukiyar al’umma
A wasu karar da ke gaban kotu da teburin DSS, ana zargin gwamnatin El-Rufai da saida kadarorin gwamnati ga mutanensa da wawurar dukiyar al’umma.
4. Jerin korafe-korafe
Tun a majalisa, aka fahimci wasu su na da korafi a kan tsohon ministan, har da wadanda aka aikawa fadar shugaban kasa, majalisar Kaduna da hukumomi.
Sauran zargin da ke wuyan El-Rufai
Rahoton ya ce ba za a rasa kuci-kucin dalilai ba daga cin mutuncin dattawan Arewa, neman soke kotunan shari’a da kuma cin amanar iyayen gidansa a siyasa.
5. Rusa kasuwanni da gidaje da kawo manufofin da za su wahalar da al’umma.
6. Cin amanar iyayen gidansa a siyasa.
7. Zargin ya bayyana Bola Tinubu da mara gaskiya.
8. Kararrarki da su ke kotu a gida da kasar waje
9. Amfani da karfi wajen murkushe abokan adawar siyasa
10. Kisan kare-dangi ga mazauna Kaduna da ganin bayan masu zanga-zanga
Halin da Nasir El-Rufai ya shiga
Nasir El-Rufai bai taba nuna ya na kwadayin Bola Tinubu ya ba shi mukami, amma daga baya ya amince zai yi aiki da gwamnati mai-ci.
A wani lamari mai kama da tuggun siyasa, ana neman hana Malam El-Rufai sake zama Minista, an samu labarin abin da ya kai ya kawo.
Asali: Legit.ng