Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Kotuna Saboda Tsoron Rashin Nasara? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Kotuna Saboda Tsoron Rashin Nasara? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wata kafar yada labarai, Igbo Times Magazine, ta rahoto a baya-bayan nan cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da dakatar da dukkan kotuna a Najeriya saboda tsoron sauke shi
  • Rahoton ya ce Tinubu ya yi nuni ga kariyar sa na shugaban kasa "sannan ya yi ikirarin cewa ya bankado wasu shaidun da ke nuna cewa an tafka magudi a bangaren shari'a"
  • Wani dandalin bincike da tantance gaskiya, Dubawa, ya binciki 'labaran' ya kuma gano an kitsa shi ne

Abuja - A ranar 26 ga watan Yuli, wata kafar yada labarai, Igbo Times Magazine, ta wallafa wani labari da ke ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi umurnin dakatar da dukkan kotunan da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, Abuja.

An rahoto cewa ya dakatar da kotunan ne saboda fargabar kada a sauke shi.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Tinubu bai dakatar da kotunan kasar ba
Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Kotuna Kan Tsoron Sauke Shi? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Labarin karya a kan Tinubu ya bayyana

Kanen labarin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dan takarar shugaban kasa Tinubu ya sanar da dakatar da dukkan kotuna a Najeriya, saboda tsoron kada a sauke shi."

Wani dandalin binciken kwakwaf, Dubawa ya binciki ikirarin.

A cewar sa, tushen labarin ba sahihi bane. Dandalin ya kara da cewar babu wata sahihiyar kafar labarai da ta tabbatar da ikirarin da mujallar Igbo Times ta yi.

Dubawa ta kuma ce ta tuntubi kakakin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Barista Felix Morka, wanda ya yi watsi da rahoton, yana mai kiranta da "shirmen banza".

Abun lura da cewa shafin da ya wallafa labarin yana yawan yada labaran karya da batarwa game da zaben shugaban kasa na 2023.

Odili bata yi wa shugaban kasa Tinubu aiki

Kara karanta wannan

Tawagar Majalisar Koli Ta Shari’a Ta Gana Da Shugaban Kasa Tinubu, Cikakken Bayani Ya Bayyana

A wani labarin, mun ji cewa Mary Peter-Odili, alkaliyar kotun ƙoli wacce ta yi murabus, ta musanta zargin nuna son kai da cin hanci da ake mata.

Maganganu sun yi yawa a soshiyal midiya cewa Misis Odili tana aiki tare da alƙalan kotun daukaka kara domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya yi nasara akan karar da jam'iyyun adawa suka shigar ta kalubalantar nasararsa a zabe.

Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa na jami'iyyar Labour Party (LP), da Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), suna kalubalantar sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu wanda Shugaba Tinubu ya lashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng