Akwai Dalili: Shugabar Matan Ta Bada Uzurin Rubuta Takardar Murabus Rana Tsaka
Hajara Wanka ta jefa kafa daya a cikin ofishin Kwamishina a jihar Bauchi, ta bar Majalisar NWC a PDP
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
- Fitacciyar ‘yar siyasar ta bar shugabancin matan jam’iyyar PDP a matakin kasa saboda ta samu mukami
- A wasikar da ta aikawa Amb. Umar Damagum, Wanka ta ce za tayi aiki da Gwamnatin jihar Bauchi
Abuja - Mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar PDP, Hajara Wanka ta ajiye aikinta, ta sauka daga kujerar da ta ke kai a Abuja.
Rahoton da aka samu daga Punch ya tabbatar da cewa Hajara Wanka ta bar majalisar NWC ne bayan ta rubuta takardar murabus.
‘Yar siyasar ta aikawa shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwaya, Ambasada Ilyasu Umar Damagum cewa ta sauka daga kujerarta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani mukamin ya fi wani
Wanka ta shaidawa Umar Damagum cewa za ta bar PDP a matakin kasa ne a sakamakon nadin Kwamishina da aka yi mata.
Gwamnan jihar Bauchi, Mai girma Bala Abdulqadir Mohammed ya nada Wanka a matsayin daya daga cikin Kwamishoninsa 23.
Jagorar matan jam’iyyar adawar ta godewa Damagum kan damar da ta samu na rike kujerar NWC a karkashin shugabancinsa.
Kwarewar da ta samu a Hedikwatar jam’iyyar PDP za ta taikmaka mata wajen yin aiki da Sanata Bala Abdulqadir Mohammed.
PDP ta karbi murabus da aka yi
Sahara Reporters ce Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ya taya Wanka murnar samun wannan mukami.
Ologunagba ya yi wa abokiyar aikinsa a sakatariyar fatan samun nasara a gwamnatin Bala Mohammed da ya zarce a ofis.
Mata a gwamnatin Najeriya
A rahoton da mu ka fitar kafin yanzu, an ji daya daga cikin ‘yan kwamitin tattalin arziki da haraji ita ce Miss Orire Agbaje.
Agbaje dalibar ilmin tattalin arziki ce a jami’ar Ibadan da ke aji hudu, ita ce shugabar @ui_taxclub, da kuma @SEIHUnibadan.
Asali: Legit.ng