Jerin Sunayen Tsofaffin Gwamnoni 5 Da Suka Shiga Kashi Na Biyu Na Ministocin Tinubu
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da kaso na biyu na sunayen mutanen da zai naɗa ministoci zuwa Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Laraba 2 ga watan Agusta.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya mika jerin sunayen ƙarin mutane 19 ga shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da misalin ƙarfe 03:15 na rana, inji rahoton The Punch.
Tsoffin gwamnoni biyar ne suka samu damar shiga cikin kashi na biyu bayan jerin sunayen ministoci 28 na farko da aka fitar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Tsoffin gwamnoni 5 da suka yi nasarar shiga jerin sunayen ministocin Tinubu kashi na biyu
1. Tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Oyetola dai shi ne tsohon gwamnan jihar Osun, wanda ya yi wa'adinsa daga shekarar 2018 zuwa 2022.
Ya sha kaye ne a yayin da ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC a hannun gwamna jihar mai ci a yanzu, Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ya gabata.
2. Tsohon gwamnan jihar Filato, Simon Lalong
Simon Lalong ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a jihar Filato. Ya yi gwamnan jihar Filato ɗin ne daga 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Sai dai Lalong ya gaza kawo kujerar gwamna da ta shugaban ƙasa a jam'iyyar APC a jihar, inda jam'iyyar PDP ta lashe duka zaɓukan da aka yi.
3. Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle
Bello Mattawale ya yi wa'adinsa matsayin gwamnan jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023.
Kamar Oyetola, Matawalle ya sha kaye a yayin da ya sake tsayawa takara domin wa'adi na biyu, a hannun Gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP.
4. Tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam
Ibrahim Geidam tsohon gwamnan jihar Yobe ne da ya shafe shekaru 10 a karagar mulki, wato daga 2009 zuwa 2019.
Ya karbi mulki ne a hannun gwamna Mamman Bello Ali, wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon ciwon hanta a jihar Florida ta ƙasar Amurka.
A yanzu haka shine Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas a Majalisar Dattawan Najeriya.
5. Tsohon Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu
Atiku Bagudu ya yi gwamnan jihar Kebbi na tsawon shekaru takwas, wato tsakanin watan Mayun 2015, zuwa watan Mayun 2023.
Bagudu ya riƙe kujerar sanata da ke wakiltar Kebbi ta Tsakiya a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, daga 2011 zuwa 2015.
Hannatu Musawa ta sharɓi kuka a lokacin da ake tantance ta a Majalisar Dattawa
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan kukan da Hannatu Musa Musawa ta sharɓa yayin da ta bayyana a zauren Majalisar Dattawa, domin a tantance ta matsayin minista daga jihar Katsina.
Emefiele: Peter Obi Ya Dau Zafi Kan Takaddamar Jami'an DSS Da Na Gidan Yari a Kotu, Ya Bayyana Matakin Da Ya Dace a Dauka
Hakan ya faru ne a lokacin da take bayar da tarihin rayuwarta, yadda mahaifinta ya taso a matsayin talaka mai ƙaramin ƙarfi.
Asali: Legit.ng