Lauya Ya Yi Barazanar Maka Umahi A Kotu Idan Ya Ki Amincewa Da Mukamin Ministan Tinubu

Lauya Ya Yi Barazanar Maka Umahi A Kotu Idan Ya Ki Amincewa Da Mukamin Ministan Tinubu

  • Wani lauya a birnin Tarayya, Abuja ya yi barazanar maka tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi
  • Lauyan mai suna Emmanuel Ekwe ya ce idan Umahi bai karbi mukamin minista ba zai fuskanci barazanar sharia
  • Ekwe ya ce ganin irin ayyukan raya kasa da Umahi ya yi a Ebonyi, asara ne ace bai karbi mukamin minista ba

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi zai fuskanci shari'a idan ya ki karbar mukamin minista da Bola Tinubu ya nada shi.

Wani lauya da ke Abuja, Emmanuel Ekwe ya ce zai maka Umahi a babbar kotun Tarayya don tilasta masa karban mukamin minista, Legit.ng ta tattaro.

Lauya na barazanar maka tsohon gwamna Umahi a kotu kan mukamin minista
Lauya Emmanuel Ekwe Ya Yi Barazanar Maka Tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi Umahi A Kotu Idan Ya Ki Amincewa Da Mukamin Minista. Hoto: Dave Umahi/Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Ekwe ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 28 ga watan Yuli inda ya ce ana bukatar kwarewar Umahi a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Sadaukar Da Kashi 50 Na Albashinsa Don Hidimtawa Talakawan Kaduna

Lauyan ya bayyana dalilansa na daukar wannan mataki

Ya ce irin gudummawar ci gaban da ya ke bayarwa ita ta ba shi daman dacewa da wannan kujerar mai daraja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ekwe ya kara da cewa kwarewar Umahi a bangarori gina al'umma da ayyukan raya kasa da ke kawo ci gaba zai fi dacewa a ba shi ministan wuta, ayyuka da gidaje.

Har ila yau, Ekwe ya ce irin ayyukan ci gaba da Umahi ya kawo wa jiharsa ta Ebonyi ba a taba samun irinshi ba a jihar tun da aka kafa ta, cewar Tribune.

Umahi na daga cikin tsoffin gwamnoni da suka samu shiga

Ya ce Umahi zai taimaka wurin tabbatar da aniyar gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu ta bangaren ayyukan raya kasa.

Tsohon Gwamna Umahi na daga cikin jerin ministoci da Shugaba Tinubu ya mika jiya Alhamis a majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Sauran tsoffin gwamnonin sun hada da na jihar Rivers, Nyesom Wike da Kaduna, Nasiru El-rufai sai kuma na Jigawa, Badaru Abubakar.

Tsohon Bidiyon Wike Na Alfahari Akan Mukamin Minista Ya Girgiza Intanet

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi alfaharin ba zai karbi mukamin minista ba a jihar.

An gano gwamnan a wani tsohon faifan bidiyo a jihar a lokacin yakin neman zabe da aka gudanar a farkon wannan shekara.

Nyesom Wike na daga cikin tsoffin gwamnonin da suka samu shiga cikin jerin ministocin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.