Bidiyo Ya Nuna Ayarin Motoccin Gwamnan Najeriya Ta Makale Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ya Mamaye Titi

Bidiyo Ya Nuna Ayarin Motoccin Gwamnan Najeriya Ta Makale Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ya Mamaye Titi

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya makale a kan hanyar Sapele saboda lalacewar hanya bayan tafka ruwan sama
  • Gwamnan ya makale ne bayan tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Benin ta jihar ta jawo ambaliya
  • A wata sanarwa, gwamnan ya ce ba za su gyara hanyoyin ba saboda gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar gyara su

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya samu cikas yayin da ambaliyar ruwa da ya mamaye kan hanya da hana shi wucewa.

Ambaliyar ruwan ya afku ne akan hanyar Sapele da ke birnin Benin a jihar bayan tafka ruwa kamar da bakin kwarya.

Gwamnan Edo Ya Makale Saboda Lalacewar Hanya A Benin
Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki Ya Makale Akan Hanya Saboda Ambaliyar Ruwa A Benin. Hoto: @d_problemsolver, @GovernorObaseki.
Asali: Twitter

Faifan bidiyon ya nuna yadda Obaseki ya makale a hanya

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, an jiyo wata murya na cewa a yada bidiyon saboda shugabanni su san ba su tsinana komai ba, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsumagiyar Tallafin Fetur Ta Bugi Gwamnoni, Ana Tunanin Rage Facakar Kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar muryar:

"Lokacin da muke ce musu su gyara hanyoyi suna ta bata lokacinsu wurin gyara ramuka a tituna.
"Sun dauka cewa talakawa ne kadai za su sha wahala, lokaci ya yi da za su gane ba talakawa kadai ba ne ke shan wahala.
"Gwamna ne a cikin motar ta gagara tafiya, ba zai iya fitowa ba saboda kunya, talaka da mai kudi na jin radadin rashin mulki na gari."

Gwamnan ya yi bayani akan abin da ya faru

Bayan zuwa wani lokaci gwamnan da mukarrabansa sun samu damar wucewa daga wurin da lamarin ya faru, Legit.ng ta tattaro.

Gwamnan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi 23 ga watan Yuli ya ce tabbas ya makale a hanyar Sapele saboda ambaliyar ruwa.

Ya ce:

"Yau ina kan hanyar Sapele bayan tafka ruwan sama, ba a wucewa a hanyar saboda ambaliya, abin da ya faru abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

"Ta yaya za a ce yankin da ke rike da kasar ta fannin tattalin arziki a wannan hali, ba mu san ta yaya za mu kirayi gwamnatin Tarayya akan gyara wadannan hanyoyin ba."

Obaseki ya ce gwamnatinsa ba za ta gyara hanyoyin Benin zuwa Auchi da Benin zuwa Sapele ba saboda gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilar gyaransu, cewar Vanguard.

Dan Majalisar Tarayya Daga Edo Ya Yi Hatsari A Hanyar Zuwa Abuja

A wani labarin, dan majalisar Tarayya a jihar Edo, Marcus Onobun ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne dalilin hatsarin mota da ta afku akan hanyarsa ta koma wa Abuja bayan halartar taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel