Ministoci: Mutane 11 da Su ka ci Karo da Cikas a Majalisa Kafin Maryam Shetty

Ministoci: Mutane 11 da Su ka ci Karo da Cikas a Majalisa Kafin Maryam Shetty

  • Akwai ‘yan siyasa ko kwararrun ma’aikata da aka yi, wanda su ka gaza zama Ministoci a gwamnati duk da shugaban kasa ya so ya nada su.
  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi ya jawo wannan magana da ya jefa tambaya a Twitter ko an taba samun wanda aka ki tantacewa.
  • Dokar kasa ta wajabtawa duk wanda aka bada sunan shi domin zama Minista ya je majalisar dattawa ya je a tantance shi, kafin ya iya shiga ofis.

A yau ne aka ji shugaban majalisar dattawa ya sanar da janye sunan Maryam Shetty daga cikin wadanda ake so su zama Ministoci.

A maimakon haka, aka maye gurbinta da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure wanda ta rike Kwamishina a gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Kafin Maryam Shetty akwai 'yan siyasar da su ka yi irin wannan rashin sa'a bayan dawowa mulkin farar hula a Najeriya a Mayun 1999.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

Rahoton nan ya na dauke da sunayen wadannan ‘yan siyasa da ba su da sa’a ko su ka yi rashin dace:

1. Bode Agusto

A lokacin da Olusegun Obasanjo ya bada sunan Bode Agusto domin ya zama Minista, ‘yan jam’iyyarsa ta PDP ne su ka ki amincewa da shi tun daga farko.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Princess Funke Adedoyin

Ana kawo sunan Princess Funke Adedoyin a cikin wanda ta samu matsala da Sanatoci, sai dai daga baya sun amince, aka kuma rantsar da ita a mulkin PDP.

Ministoci
Olabode Agusto da Udo Udoma sun taba samun matsala wajen zama Ministoci Hoto: Olabode Agusto
Asali: Twitter

3. Babalola Borishade

An yi ta kokarin ganin Farfesa Babalola Borishade ya zama Minista a 2003 amma hakan bai yiwu ba, majalisar dattawa ba ta yarda da shi ba sai a Mayun 2004.

4. Bayo Yusuf

Shi ma Bayo Yusuf ya samu irin wannan matsala a majalisa, da aka ki tantance shi, sai dai Obasanjo ya bada sunan Segun Mimiko ya zama Minista daga Ondo.

Kara karanta wannan

Ministoci: Sanatoci sun Tantance Mutum 46, Jami’an Tsaro na Binciken Ragowar 2

5. Udoma Udo Udoma

Shi kuwa Udoma Udo Udoma ya ki yarda ya karbi Ministan ne da ya lura karamar kujera za a ba shi a FEC, sai ya zabi ya rike matsayinsa na Sanata a 1999.

6. Dr. Obadiah Ando

A 2011, Sanatocin Taraba su ka hada-kai su ka hana a sake tantance Dr. Obadiah Ando a majalisa, daga gida kuma dattawan Taraba su ka nuna ba su tare da shi.

7. Godsday Orubebe

Godsday Orubebe ya gamu da cikas ne kafin a tantance, daga nan kuma aka gagara ba shi ofis saboda rikicin siyasar Delta da sabaninsa da gwamnatin jiha.

Amma daga baya Ummaru ‘Yar’adua ya rantsar da shi a matsayin Ministan harkoki na musamman, a 2008 sai ya zama karamin Ministan harkokin Neja-Delta.

8. Bitrus Boka Ushe

Shugabannin jam’iyyar PDP Mutanen Kebbi su ka hana Bitrus Boka Ushe daga Kudancin Kebbi ya zama Minista, dole aka maye gurbinsa da wani dabam.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

9. Olusegun Aganga

A shekarar 2010, PDP ta reshen Legas ta hana a ba Segun Aganga kujerar Minista, ta ce ba a jihar aka haife shi ba, daga baya ya rike Ministan kudi da na kasuwanci.

10. Akinwumi Adesina

Ana zargin Dr. Akinwumi Adesina ya ki kai kan shi gaban majalisa ne saboda tunanin za a nada shi karamin Minista, haka ya jawo jinkiri kafin a rantsar da shi.

11. Ahmad Ibetto

A 2015, Muhammadu Buhari ya turawa majalisa sunan Ahmad Ibeto, kwatsam sai aka ji ya maye gurbinsa da Abubakar Bwari wanda shi ya zama Ministan.

"Ba a saba ji ba, abin kunya ne"

An ji labari cewa wasu 'yan jam'iyyar APC su na zargin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya je neman kujerar Minista a gwamnati.

Kungiyar ta ce Dr. Jonathan ya yi shugaban kasa na shekaru shida, ya nada tulin Ministoci, amma yanzu ya damu da kujerar da APC za ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng