A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

  • Ana ta kishin-kishin cewa nan da ‘yan awanni za a san wadanda za su zama Ministoci a Najeriya
  • Bola Ahmed Tinubu zai aikawa majalisar dattawa sunayen wadanda yake so ya yi aiki da su a FEC
  • Rahoto ya zo cewa shugaban Najeriyan ya janye sunayen wasu da ya yi tunanin ba mukamin da farko

Abuja - Kwanaki hudu su ka rage a doka domin fitar da sunayen Ministoci, har yanzu Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai kafa majalisar zartarwa ba.

Wani rahoto da Vanguard ta fitar ya bayyana cewa a cikin makon nan da aka shiga, majalisar dattawa za ta karbi sunayen Ministocin da za a tantance.

Sai dai har zuwa yanzu, majiyoyi sun shaida cewa jerin mutanen da shugaban kasar yake so su zama Ministocinsa bai kai teburin shugaban majalisa ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Shugaba Tinubu
Ana jiran Shugaban kasa ya nada Ministoci Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ana yi wa jerin garambawul a Aso Rock

Ana tunanin shugaban kasa ya aikawa Sanatoci wasika a makon da ya gabata, amma a halin yanzu ana yin wasu kwaskwarima ne a mintin karshe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce an canza sunayen wasu daga cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya bada na wadanda yake so su zama Ministocinsa daga Jihohi shida.

Legit.ng Hausa ba ta da masaniya a kan jihohin da aka canza sunayen, sai dai hakan ba bakon abu ba ne saboda runtsi na siyasa, addini na neman kwararru.

Wata majiya ta ce saura kiris a sanar da sunayen zababbun Ministocin, amma ganin Abdullahi Umar Ganduje a ciki ya jawowa shugaban Najeriyan suka.

Majalisar dattawa ta shirya

Majalisar dattawa ta ce ana aiko mata wasika, za ta fara tantance mutanen. Shugaban kwamitin labarai, Sanata Yemi Adaramodu ya fadawa Tribune.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Za a Ƙara Cin Wahala, Masani Ya Yi Hasashen Shekarar Samun Sauƙi

A game da batun Ministocin da za a nada, Akawun majalisa ya ce takarda ba ta shigo hannunsu daga fadar shugaban kasa ba, hakan ya sa ba a karanto jerin ba.

Har zuwa ranar Juma’ar da ta wuce ana ta canza wasu sunaye ne, amma a makon nan mai bada shawara kan harkokin majalisar dattawa zai mika takardar.

Ganduje ya canza lissafi a APC

Da farko an yi tunanin ba Ganduje kujerar Minista, amma murabus da Abdullahi Adamu ya yi, ya jawo aka fara maganar tsohon Gwamnan ya jagoranci APC.

Hakan ya jawo sabani a jam’iyyar APC inda wasu su ke ganin daga Arewa maso tsakiya ya dace a samu magajin Adamu, ana goyon bayan Tanko Al-Makura.

Takardar Salihu Luman

Rahoto ya zo cewa shugaba a jam'iyya, Salihu Luman ya rubutawa Kungiyar PGF wasika, ya ce Gwamnoni su sake yin tunani game da shugabancin APC.

Duk da ya yaki Abdullahi Adamu, Lukman ya ce ba ayi wa Bola Tinubu da jagororin jam'iyya mai mulki adalci idan aka ba Abdullahi Ganduje rikon APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng