Cire Tallafi: Akpabio Ya Ce Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Albashin Ma’akatan Najeriya

Cire Tallafi: Akpabio Ya Ce Gwamnatin Tinubu Za Ta Kara Albashin Ma’akatan Najeriya

  • Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta karawa ma’aikata albashi
  • Ya ce karin albashin wani yunkuri ne na gwamnatin Tinubu wajen ganin ta ragewa ‘yan Najeriya radadin da cire tallafin man fetur ya saka su a ciki
  • Akpabio ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin ta Tinubu na da karfin da za ta iya biyan sabon albashin da ake son karawa

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta kara albashin ma’aikata domin rage musu radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, da tawagarsa a ofishinsa da ke Abuja ranar Talata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

Akpabio ya ce Tinubu zai karawa ma'aikata albashi
Akpabio ya ce Tinubu zai kara albashin ma'akata domin rage radadin cire tallafin man fetur. Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Dalilin da ya sa Tinubu ya cire tallafin man fetur – Akpabio ya yi bayani

Shugaban na Majalisar Dattawa, ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya na sane da irin wahalhalun da ‘yan kasa ke sha sakamakon cire tallafin man fetur.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce cire tallafin na daga cikin matakan da gwamnati mai ci ke bi wajen ganin ta yaki cin hanci da rashawa, musamman in aka yi duba da yadda ya yi wa bangaren tallafin man katutu.

Ya kara da cewa ba domin cire tallafin da aka yi ba, Najeriya ba za ta iya ci gaba da gudanar da al’amuranta a matsayin kasa ba.

Akpabio ya kuma jaddada cewa gwamnati tana da karfin da za ta iya biyan sabon albashin da ake yunkurin karawar.

Gwamnan Ekiti ya yabawa Akpabio kan nasarorin da ya samu

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

Da yake jawabi, Gwamna Oyebanji ya yabawa shugaban Majalisar Dattawan bisa nasarorin da ya samu a wata dayan da ya shafe yana shugabanci.

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin samun goyon bayansa ga shugaban na Majalisar Dattawa ta 10 kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

Haka nan ya bayyana cewa a shirye yake ya yi hadaka da majalisar wajen ciyar da Najeriya gaba.

Majalisar za ta bayyana sunayen ministocin Tinubu a yau Laraba

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton cewa a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli ne Majalisar Dattawan Najeriya za ta bayyana sunayen ministocin gwamnatin Tinubu.

Hakan dai na zuwa ne bayan jiran da ‘yan Najeriya suka dade suna yi na ganin an nada sabbin ministoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng