Jam'iyyar Labour Ta Buƙaci a Kori Shugaban INEC, Sannan a Gudanar Da Bincike a Hukumar

Jam'iyyar Labour Ta Buƙaci a Kori Shugaban INEC, Sannan a Gudanar Da Bincike a Hukumar

  • Jam'iyyar Labour ta buƙaci a kori shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu
  • Hakanan ta kuma nemi a gudanar da bincike kan shige da ficen kuɗaɗe a hukumar ta INEC na lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe
  • Jam'iyyar ta Labour ta kuma buƙaci a gudanar da bincike kan wasu manyan ma'aikata na hukumar zaɓen

Abuja - An buƙaci a gaggauta korar Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa rawar da ya taka a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Darakta janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ta Labour, Akin Osuntokun ne ya yi wannan kira a wajen wani taro a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja kamar yadda The Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

An nemi a kori shugaban hukumar zabe daga mukaminsa
Jam'iyyar Labour ta bukaci a kori Farfesa Mahmood daga shugabancin INEC. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Ya nemi a gudanar da binciken ƙwaƙwaf a hukumar ta INEC

Osuntokun ya kuma buƙaci da a gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan duk wasu kuɗaɗe ko gudummawar da hukumar ta samu kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce baya ga naira biliyan 300 da aka ware daga lalitar ƙasa, akwai ƙarin wasu kuɗaɗe da kayayyaki da aka samu daga wasu hukumomi na ƙasashen waje.

Hakan dai na zuwa ne watanni biyar da gudanar da zaɓen 25 ga watan Fabrairu, inda hukumar ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A lokacin zaɓen, Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726 inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar mai ƙuri'u 6,984,520, da takwaransa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda ya samu ƙuri’u 6,101,533.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanar Cewa 'Yan Najeriya 12m Za Su Rika Samun N8,000 Kowane Wata Har Tsawon Wata Shida, Jama'a Sun Yi Martani

Sai dai Atiku da Obi sun yi watsi da sakamakon zaɓen, saboda zargin cewa an tafka maguɗi, inda daga nan suka garzaya kotun sauraron ƙararrakin zaɓe domin kai koke.

Ya nemi a hukunta wasu manyan jami'an INEC

Osuntokun ya shaidawa manema labarai cewa, duk shaidun da jam’iyyun PDP da Labour suka gabatar, sun tabbatar da zargin da ake yi na cewa an tafka magudi a zaɓen.

Sannan ya yi kira da a ɗauki matakin hukunta kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye.

Ya kuma nemi a hukunta sauran manyan ma’aikatan gudanarwa na hukumar kan zargin haɗa baki da su da aka yi kamar yadda The Cable ta wallafa.

Osuntokun ya kuma ce a daina duk wata barazana ga masu sanya ido na Tarayyar Turai kan rahotannin da suka bayar kan zaɓen da ya gabata.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Kasa Adamu Ya Ce Ba Tinubu Ba Ne Dan Takararsa a Zaben Fidda Gwani, Ya Bayyana Wanda Ya Marawa Baya

Tinubu ya ba gwamnoni 36 izinin kawo waɗanda suke so a ba muƙami

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa gwamnonin Najeriya izinin kawo mutanen da suke so a bai wa muƙami a jihohinsu.

Ya bayyana hakan ne yayin taronsa da ƙungiyar gwamnonin Najeriya a fadar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng