Shugaban APC Na Kasa Adamu Ya Ce Bai Goyi Bayan Tinubu Ba a Zaben Fidda Gwani, Ya Ambato Sunan Dan Takararsa

Shugaban APC Na Kasa Adamu Ya Ce Bai Goyi Bayan Tinubu Ba a Zaben Fidda Gwani, Ya Ambato Sunan Dan Takararsa

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce bai goyi bayan Shugaba Tinubu ba a lokacin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar
  • Adamu ya bayyana ɗan takarar da ya goyawa baya a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa shi ne tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
  • Ya yi nuni da cewa ya yi aiki tuƙuru domin nasarar Tinubu a babban zaɓen 2023 duk da ba shi ba ne ɗan takarar da yake so a lokacin zaɓen fidda gwanin

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi ba ne ɗan takarar da yake goyon ba a yayin da ake tunkarar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.

Adamu ya yi nuni da cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan shi ne zaɓinsa, amma ya marawa Tinubu baya bayan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Shirya Karban Gwamnonin PDP 5 Da Zaran Sun Shirya Sauya Sheƙa Zuwa Cikinta

Abdullahi Adamu ya ce ba Tinubu ba ne zabinsa
Abdullahi Adamu ya ce Ahmad Lawan ya marawa baya ba Tinibu ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Sen. Abdullahi Adamu-APC National Chairman
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, lokacin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise News.

Shugaban na jam'iyyar APC ya kuma bayyana cewa yana da ƴancin goyon bayan duk wanda yake so kafin Shugaba Tinubu ya yi nasara a zaɓen fidda gwanin na shekarar 2022.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Dama abinda ku ƴan jarida ku ke nema kenan. Eh da gaske ne a lokacin na gabatar bayani ga mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), inda sunan Ahmad Lawan ya fito."
"Wannan kafin ayi babban taron jam'iyya ne. Don haka abubuwa da dama sun faru daga wannan lokacin zuwa ranar da aka gudanar da babban taron sannan kun ga abubuwan da aka yi a wajen taron. Ina wajen inda na jagoranci babban taron jam'iyyar."
"Kwana ɗaya bayan zaɓen, na jagoranci gaba ɗaya ƴan kwamitin (NWC) zuwa gidan Tinubu a Asokoro, inda na tabbatar masa da goyon bayan mu da cewa za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da shi domin tallata shi a wajen ƴan Najeriya. Mun lashe zaɓen, a maimakon a yabe mu sai aka koma ana hantarar mu."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Adadin Yawan Ministocin Da Tinubu Zai Nada Ya Bayyana

A wani labarin kuma, an bayyana adadin yawan ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai naɗa a gwamnatinsa.

Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ya bayyana cewa shugaban ƙasar yana da hurumin naɗa ministoci 34 zuwa 42 a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel