Gwamnan Zamfara, Lawal Dare Ya Bayyana Yadda Ya Samu Lalitar Gwamnati Sisi Babu, Ya Koka Da Mulkin Matawalle
- Gwamnan jihar Zamfara, Lawal Dare ya bayyana yadda ya samu asusun gwamnatin jihar ko taro babu
- Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawa da kwararru 'yan jihar da ke zama a birnin Tarayya Abuja
- Ya ce lokacin da ya shiga ofishin gidan gwamnati ya tarar da bashin albashin ma'aikata har na watanni uku
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal Dare na Zamfara ya bayyana cewa bai samu ko sisin kwabo ba a asusun gwamnatin jihar.
Lawal ya bayyana haka ne yayin ganawa da kwararru 'yan jihar da ke Abuja a ranar Laraba 12 ga watan Yuli.
Ya ce ya tsinci jihar cikin mawuyacin hali na rashin kudi lokacin da ya shiga gidan gwamnati, cewar Daily Trust.
Ya ce ya gaji mulki babu komai a lalitar gwamnati
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Mun gaji gwamnatin nan a cikin mawuyacin hali, lokacin da muka karbi mulki babu ko sisi a asusun gwamnati.
"Jiha ce da ba mu gaji komai ba sai abubuwa marasa kyau."
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin amsa tambayoyi daga kwararrun, inda ya ba su tabbacin daidaita komai yadda ya dace, Naija Times ta tattaro.
Ya kara da cewa lokacin da ya shiga ofishin gidan gwamnati ya tarar da bashin albashin ma'aikata na watanni uku, cewar PM News.
Ya ce ya rage ma'aikatu a jihar saboda yawan kashe kudade
Dauda Lawal ya ce sisi babu a asusun gwamnatin da za a biya wadannan ma'aikata, dadi da kari ga dalibai suna zaune saboda kudaden jarabawar WAEC.
Bangaren rage yawan kashe-kashen kudade a gwamnati kuwa, ya ce sun dauki matakai a kan haka.
Ya ce lokacin da ya zo, ya tarar da ma'aikatu 28 a jihar, wanda yanzu ya rage su zuwa 16 don rage yawan barnar kudade.
Naira N4m Kacal Na Tarar A Asusun Gwamnatin Zamfara, Gwamna Lawal Dare
A wani labarin, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa N4m kacal ya samu a asusun gwamnatin jihar.
Ya ce ya gaji gwamnatin ba tare da samun wani abin kirki da zai aiwatar da harkokin gwamnati ba.
Ya koka kan yadda gwamnatin da ta shude ta lalata harkokin gwamnatin jihar cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng