Makusancin Tinubu Ya Samu Babban Mukami A Majalisa Yayin Da Akpabio Ya Nada Sabbin Mukamai

Makusancin Tinubu Ya Samu Babban Mukami A Majalisa Yayin Da Akpabio Ya Nada Sabbin Mukamai

  • Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya nada sabbin shugabannin kwamitoci daban-daban a majalisar
  • Sanata Solomon Adeola wanda ya kasance yaron Shugaba Tinubu ne ya samu babban mukami a majalisar
  • An nada Adeola shugaban kwamitin kasafi na majalisar, wanda na daya daga cikin kwamitin da ake wawansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya nada shugabannin kwamitoci da dama a majalisar.

Kwamitocin sun hada da na da’a da kula da jama’a da kararrakin jama’a da kuma rabon kudade wato kasafi na majalisar.

Yaron Tinubu Ya Samu Babban Mukami A Majalisa Yayin Da Akpabio Ya Nada Sabbin Mukamai
Sanata Solomon Adeola, Shugaban Kwamitin Kasafi. Hoto: Sanata Solomon Adeola.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa, Akpabio ya sanar da nadin ne a yau Talata 11 ga watan Yuli yayin zaman majalisar a Abuja.

Makusancin Tinubu ya samu babban mukami a majalisar Dattawa

An nada Sanata Solomon Adeola a matsayin shugaban kwamitin kasafi, yayin da Sanata Ahmed Wada daga jihar Nasarawa zai shugabanci kwamitin da ya shafi kula da jama'a.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Adeola wanda aka fi sani da 'Yayi' ya kasance na hannun daman Shugaba Bola Tinubu, cewar gidan talabijin na Channels.

Ana sa ran, Yayi zai zama garkuwan gwamnatin Tinubu a cikin majalisar da kuma wasu abubuwa da suka shafi majalisar.

Dan jarida Journalist KC ya wallafa faifan bidiyo inda ya ce an nada Sanata Ali Ndume a matsayin mataimakin shugaban kwamitin kasafi na majalisar.

Kwamitocin da ake wawarsu a majalisar saboda alkairin da ke ciki

Akwai wadansu mukamai a majalisar da ko wane mamba ke son shugabanta ko kuma kasancewa a cikin mambobin kwamitin.

Kwamitin da ya yafi ko wane shi ne na kasafi a majalisar wanda ake kai ruwa rana don samun wannan dama, Premium Times ta tattaro.

Sauran sun hada da kwamitin ma'adanan man fetur da kudi da kuma sadarwa da fasa kwauri da tsaro da sauransu.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Sabin Nade-Nade 2 Masu Muhimmanci

Punch ta ruwaito cewa a makon da ya gabata, Godswill Akpabio ya kai wa Shugaba Tinubu ziyara don tattauna yadda tsarin kwamitocin za su kasance.

Hakan bai rasa nasaba da yadda mambobin ke kokarin kasancewa a cikin manyan kwamitoci da suke ganin akwai samu.

Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar Da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

A wani labarin, shugaban majalisar Dattawa a Najeriya, Godswill Akpabio ya sanar da sabbin shugabannin majalisar.

Akpabio ya ce an zabi dukkan mambobin ne ta hanyar maslaha ba tare da wani tashin hankali ba.

Daga cikinsu akwai Sanata Opeyemi Bamidele a matsayin shugaban masu rinjaye yayin da Dave Umahi ya kasance mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel