Zaben 2023: Dattijuwa Ta Tsinewa Peter Obi Da Jam'iyyar Labour, Ta Bayyana Dalilai

Zaben 2023: Dattijuwa Ta Tsinewa Peter Obi Da Jam'iyyar Labour, Ta Bayyana Dalilai

  • Wata tsohuwa 'yar shekara 74 ta yi Allah wadai da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour da ita kanta jam'iyyar
  • Tsohuwar mai suna Chinyere Obi wacce Kanal ce mai ritaya ta bayyana yadda ta samu harbin bindiga yayin zabe a jihar Imo
  • Ta ce ta yi dana sanin shiga jam'iyyar ganin yadda ta kusa rasa kafarta amma babu wanda ya taba neman inda take

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wata tsohuwar Kanal mai ritaya, Chinyere Obi ta tsinewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour da kuma jam'iyyar kanta.

Tsohuwar mai shekaru 74 ta koka kan yadda jam'iyyar ta manta da ita bayan ta sha harbi a kokarin kare martabar jam'iyyar a jihar Imo.

Tsohuwa Mai Shekaru 74 Ta Yi Allah Wadai Da Peter Obi Da Jam'iyyarsa Akan Zaben 2023
Kanal Chinyere Obi da Peter Obi. Hoto: Segun Adeyemi/Original and Mr Peter Obi/Facebook.
Asali: UGC

Obi wacce mamba ce a jam'iyyar ta bayyana haka ne ga Legit.ng a Abuja a yau Alhamis 6 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

Tsohuwar ta bayyana yadda ta sha bakar wahala a zaben 2023 akan Peter Obi

A cewarta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Dole ne siyar da motata N1.5m a watan Yuni don jinyar harbin da aka yi min, a shekaru na 74 ace sai na siyar da kaya na don yin jinya."

Ta ce ita Kanal ce mai ritaya ta na da fansho ba ta roki wani abu daga dan takarar shugaban kasar ba.

Matar ta koka kan yadda babu wani dan jam'iyyar da yazo dubata a asibitin yayin da take jinya.

Ta ce ta yi yaki saboda Obi da kuma matasan Najeriya don samun ingantacciyar rayuwa, ta ce ba ta bukatar komai saboda ita 'yar Burtaniya ce da dukkan 'ya'yanta,

Obi ta ce ta gamu da tsautsayin ne yayin da ta yi kokarin kare wata rumfar zabe a karamar hukumar Ideato ta jihar Imo, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

“Sharadi Ba Za Ka Yi Mun Kishiya Ba”: Budurwa Ta Yi Alkawarin Baiwa Duk Wanda Ya Aureta Gida, Mota da Miliyan 50 a Bidiyo

Ta koka yadda babu wani jam'iyyar Labour da ya zo duba ta

Ta ce:

"Ban ankara ba sai naji harbi a kafata, ga shi ina da ciwon sukari, hakan zai iya sa a yanke min kafa.
"Amma babu wanda ya zo duba ni daga Aburi har Peter Obi bai turo ko sakon jaje ba.
"Na yi dana sani, na tsinewa ranar da na shiga jam'iyyar Labour, ina zama na a PDP, lokacin da Peter Obi ya shiga jam'iyyar Labour sai na bi shi."

A karshe ta yabi Shugaba Tinubu inda ta ce ta na sa ran zai gyara kasar Najeriya, ta roke shi da ya kawo karshen rashin tsaro musamman a Kudu maso Gabashin kasar.

Har Yanzu Peter Obi Ya Fi Tinubu, Atiku Da Saura, In Ji Obasanjo

A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa har yanzu babu wanda ya kai Peter Obi cancanta.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Maimaita Tufafin Da Mataifiyarta Ta Sanya Shekaru 29 Da Suka Gabata a Ranar Aurenta

Ya ce dan takarar jam'iyyar Labour ya fi Bola Tinubu da Atiku Abubakar cancantar shugabancin kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa Obasanjo ya bayyana haka ne yayin ganawarshi da dan jarida Chude Jideonwu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.