Kungiyar PDP Ta Ki Aminta Da Tambuwal A Matsayin Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dattawa, Ta Bada Dalili

Kungiyar PDP Ta Ki Aminta Da Tambuwal A Matsayin Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dattawa, Ta Bada Dalili

  • Wata kungiyar PDP ta ƙi amincewa da zaɓin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a matsayin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa
  • Kungiyar da ake kira da 'Concerned PDP League' (CPDPL), ta ce ba za ta bai wa Aminu Tambuwal goyon bayanta ba, saboda ba za a iya amincewa da shi ba
  • Shugaban na ƙungiyar CPDPL, Daboikiabo Warmate, ya ce kamata ya yi PDP ta zaɓo shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawan daga jihar Filato

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata ƙungiyar 'yan jam'iyyar PDP mai suna 'Concerned PDP League', ta ce ba za ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ba.

Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa, Shugaban ƙungiyar ta CPDPL, Daboikiabo Warmate, ya ce ba za su amince da Tambuwal a karo na biyu ba, bayan sauya sheƙa da ya yi zuwa jam’iyyar APC da ya yi a lokacin da yake shugaban Majalisar Wakilai.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Sanata Ya Faɗi Mutum 2 Tal da Suka Jawo Atiku Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Zaɓen 2023

Wata kungiyar PDP ta ki aminta da Tambuwal a majalisar Dattawa
Kungiyar CPDPL ta ce ba ta yarda a bai wa Tambuwal shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa ba. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Kungiyar ta ce Tambuwal bai cancanci zama shugaban marasa rinjaye ba

Warmate ya kuma ƙara da cewa duba da irin abinda Amimu Tambuwal ya yi a baya, ba shi da karfin gwiwar iya zama shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan ta 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Warmate, ya kamata jam'iyyar PDP ta miƙa kujerar shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan zuwa wata jiha a Arewa ta Tsakiya, kamar jihar Filato.

Warmate ya ce ko kaɗan burin da Tambuwal ɗin yake da shi na neman kujerar shugaban marasa rinjaye ba zai cika ba, saboda abubuwan da ya yi a baya.

A cewarsa:

“Abin takaici ne da kuma mamaki da na karanta a cikin jarida cewa Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP yana son zama shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa ta 10.”

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

“Mutumin da a shekarar 2014 ya samu shugabancin Majalisar Wakilai da muka ba shi, amma sai ya koma wata jam’iyyar. Wannan mutumin kuma shi ne ya sake dawowa jam’iyyar.”
“Yanzu, yana son ya zama shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa ta 10, ba za mu ba shi goyon baya ba.
"Shekaru aru-aru, shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, amma ya kasa yin magana game da murkushewa da wahalar da 'yan Najeriya da ake yi."

Kungiyar ta ce Tambuwal bai taka rawar gani ba a shugabancin jam'iyyar adawa

A rahoton Voice of Nigeria, ƙungiyar ta kuma buƙaci shugaban wucin gadi na jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, da kada ya rattaɓa hannu kan duk wata takarda da ta gabatar da Tambuwal a matsayin shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa ta 10.

“Tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP bai yi wani kataɓus ba a lokacin da yake shugaban jam’iyyar adawa.”

Kara karanta wannan

Babban Rashi: Allah Ya Yi Wa Fitaccen Ɗan Siyasa Kuma Makusancin Atiku Abukar Rasuwa, Bayanai Sun Fito

“Abin ya isa haka nan, ba za a riƙa amfani da ’yan PDP ana watsi da su ba daga baya ba.”
“Jam’iyyar PDP ce ba jam'iyyar wasu shafaffu da mai ko masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ba, abin da muke so su sani ke nan.”
“Ba za mu bari mambobi, shugabanni ko ko wani shugaba, su yi amfani da jam’iyyar su watsar da ita a lokacin da suka ga dama ba, a’a! Wannan ba mai yiwuwa ba ne. Muna da buƙatar mu faɗa musu gaskiya.”

Atiku ya nemi 'yan Najeriya da su yi wa ƙasar addu'a

Legit.ng ta kawo muku a baya, labarin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya roƙi 'yan Najeriya da su yi wa ƙasar addu'ar samun albarka da ci gaba.

Atiku ya yi roƙon ne a cikin saƙon taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar bikin babbar sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel