Bikin Sallah: San Barka Yayin Da Peter Obi Ya Ba Da Kyautar Kudi Don Gyaran Masallatai
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi bikin murnar babbar sallah tare da Musulmai
- Obi yayin ziyararsa ga al'ummar Musulmai a Awka da Onitsha a watan Afrilu ya yi alkawarin gyara musu masallatai
- Obi a jiya Laraba 28 ga watan Yuni ya cika alkawari tare da basu cak na kudi don gyaran masallatan guda biyu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Anambra - Dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ba da cak na kudi ga shugabannin al'ummar Musulmai da ke Awka da Onitsha a jihar Anambra.
Peter Obi ya ce wannan kyauta ya yi ta ne don cika alkawarin da ya dauka a baya, yayin da ya taya al'ummar Musulmai bikin sallah babba, cewar Legit.ng.
Obi ya taya al'umar Musulmai murnar sallah
Obi, mai shekaru 61 ya rubuta a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 28 ga watan Yuni kamar haka:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Yau na karbi bakwancin al'ummar Musulmai a gida na da ke Onitsha saboda murnar bikin sallah.
"Na kuma mika musu cak na kudi ga al'ummar Musulmai na Awka da Onitsha kamar yadda na yi alkawari a baya na gyaran masallatansu."
Peter Obi ya yi alkawarin ba da taimako don gyaran masallatai
Bayan wannan kyautatawa, magoya bayan Peter Obi, har ma da wadanda ba sa tare da shi a siyasa sun yabi tsohon gwamnan Anambra, Tribune ta tattaro.
Hadimin tsohon shugaban kasa Buhari, @Bashir Ahmad ya ce:
"Mun gode."
"Abin da kayi abin a yaba ne, ka ci gaba da aikin alkairi, hada kan kasa shi ne mafita."
"Peter Obi ya na da cika alkawari."
"Hotunan sun yi kyau, Allah ya saka maka da gyaran masallaci da ka yi."
"Madalla da abin da kake yi kullum, abin takaici duk yadda ka dauki sauran addini da yanki, tsanarsu a fili suke nunawa Ibo, ubangiji ya bamu ci gaba da zaman lafiya."
Peter Obi Ya Soki Rusau Din Kano, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Wankin Babban Bargo
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya caccaki Gwamna Abba Kabir na Kano kan rusau.
Peter Obi ya ce tsarin da ake bi wurin rusau din babu tausayawa a ciki ganin yadda ake asarar dukiya.
Asali: Legit.ng