Nuhu Ribadu Da Sauran Manyan Jiga-Jigan Da Suka Tarbi Shugaba Tinubu a Legas

Nuhu Ribadu Da Sauran Manyan Jiga-Jigan Da Suka Tarbi Shugaba Tinubu a Legas

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan ya kwashe kwanaki bakwai a ƙasar Faransa wajen taro da birnin Landan a wata ƴar gajeruwar ziyara.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban ƙasar ya iso birnin Legas a ranar Talata, 27 ga watan Yuni, inda ya samu gagarumar tarba daga wajen muƙarraban gwamnatinsa da magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Manyan jiga-jigan da suka tarbi Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu ya samu kyakkyawar tarba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

A cewar wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu, Dele Alake ya fitar manyan jiga-jigan da suka tarbi shugaban ƙasar sun haɗa da:

Nuhu Ribadu

Mai bada shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA) Nuhu Ribadu, yana ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da suka tarbi shugaɓa Tinubu a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke birnin Legas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bayyana Ranar Da Shugaba Tinubu Zai Dawo Gida Najeriya

Babajide Sanwo-Olu

Gwamnan jihar Legas shi ne mai masaukin baƙi ga shugaban ƙasar duk kuwa da cewa Legas gidan shugaban ƙasar ne.

Sanwo-Olu an daɗe ana masa kallon na kusa da Shugaba Tinubu saboda kyakkyawar dangantakar da ke a tsakaninsu.

Femi Gbajabiamila

Dele Alake ya kuma bayyana cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, yana daga cikin masu tarbar shugaban ƙasar.

Sanatocin Legas da ƴan majalisu

A cewar Dele Alake, Sanatoci uku da ƴan majalisar wakilai na jihar Legas, sun tarbi shugaban ƙasar bayan ya iso daga birnin Landan.

Sanatocin guda uku waɗanda su ke wakiltar jihar Legas a majalisar dattawa sun haɗa da Idiat Adebule (Legas ta Yamma), Tokunbo Abiru (Legas ta Gabas), da Wasiu Eshinlokun (Legas ta tsakiya).

Magoya bayan APC

Shugaban ƙasar ya kuma samu tarbar wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar APC waɗanda suka fito domin yi masa tarba mai kyau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Fasa Dawowa Gida Najeriya Daga Faransa, An Bayyana Inda Jirginsa Zai Shilla

Shugaba Tinubu dai shi ne jagoran jam'iyyar APC na ƙasa tun kafin ya zama shugaban ƙasa.

Bayan Kwanaki a Kasar Waje, Shugaba Tinubu Ya Diro Najeriya

Rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya iso Najeriya daga ziyararsa ta farko da ya kai zuwa ƙasar waje tun bayan da ya zama shugaban ƙasar Najeriya.

Shugaba Tinubu ya iso Najeriya ne daga birnin Landan a ranar Talata, 27 ga watan Yuni bayan ya shafe kwanaki bakwai ba ya cikin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel