Dan Takarar Shugaban Kasa Na SDP Ya Yi Hasashen Yadda Shari'ar Atiku, Obi Da Tinubu Za Ta Kare A Kotu
- Barista Adewole Adebayo, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar SDP, ya fuskanci zazzafan martani daga masu amfani da Intanet
- Masu amfani da yanar gizo sun caccake shi ne saboda hasashensa game da shari'ar da ke gudana a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa
- Dan takarar shugaban kasar na SDP a hasashensa, ya nuna shakku kan yiwuwar samun nasarar Peter Obi da Atiku Abubakar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar SDP, Barista Adewole Adebayo, ya yi hasashe kan shari'ar da ke gudana a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Tuwita a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, Adebayo ya nuna rashin kwarin gwiwar cewa wadanda suka shigar da kara, wato Atiku Abubakar na PDP, da Peter Obi na Jam’iyyar Labour da wuya ne a yi musu adalci.
Kamar yadda ya rubuta:
"Kamar yadda @atiku @OfficialPDPNig @PeterObi @NgLabour suka rufe kararrakinsu a kotun kararrakin zabe, za a iya cewa sun kara wasu sabbin abubuwa a cikin shari'ar mu amma babu komai a bangaren adalci:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
(a) ba wani abu (b) babu wata hujja ( c) tabbas za a gamu da rashin nasara koda kuwa @inecnigeria ba ta da wani kwakkwaran lauya."
Ya kara da cewa:
"Shin yanzu korar da za a yi wa wadannan kararrakin na nufin kawo karshen aikin da ya rataya a wuyan 'yan siyasar Najeriya wajen cimma matsaya mai karfi kan cewa al'ummar Najeriya sun cancanci samun zabe mai tsafta, bayyananne, sahihi ba tare da tada hankali ba? don haka dole ne mu hadu."
Masu amfani da yanar gizo sun yi martani kan rubutun nasa
Biyo bayan wadannan kalamai nasa, wasu 'yan Najeriya sun yi amfani da sashin sharhi na shi baristan don bayyana ra'ayoyinsu.
@rilwan_ola01 ya ce:
"Zai fiye maka kyau ka cire wannan ESQ dake gaban sunanka, don kada ka ƙara ɓata sunan sashin shari'a.
"Takardar karatunka a matsayin lauya har yanzui ta na nan lafiya lau, sai dai ingancin matakan da ka bi wajen samun wannan damar shi ne abin dubawa."
Wani mai bincike kan da'a kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Victor Wolemonwu ya ce:
"Esq din mu ya gamsu da gurbataccen tsarin da ake kai ta yanda har yake kokarin kare shi da da ba shi goyon baya, a ganinsa shi komi lafiya lau, babu abin da ya lalace! Haha!"
Jackson Ude, kwararre kan harkokin sadarwa ya ce:
"ESQ da ka sanya a gaban sunanka sai ta mayar da kai wani wawa. Wani lokacin yin shiru yafi. Dan takarar shugaban kasa na SDP din banza kawai!"
Peter Obi ya bayyana ra'ayinsa kan rushe-rushen da Abba Gida Gida yake yi
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Amince Da Korafin Atiku Akan Tinubu Na Takardar Shaidar Jami'ar Chicago Da Kuma Bautar Kasa NYSC
Legit.ng a by ta kawo muku labari kan martanin da dan takarar shugabancin kasa naa jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi dangane da rusau da gwamnan Kano, Abba Gida Gida ke yi.
Obi ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta iya yi wa wasu daga ciki da suka yi ginin bisa kuskure uzuri domin kaucewa batun rusau din.
Asali: Legit.ng