An Samu Mukamai 2000 da Za a Cusa ‘Yan APC da Masoyan Tinubu a Gwamnatin Tarayya

An Samu Mukamai 2000 da Za a Cusa ‘Yan APC da Masoyan Tinubu a Gwamnatin Tarayya

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauke shugabannin majalisun da ke kula da hukumomin tarayya
  • Ana lissafin cewa an samu gurabe kusan 2000 da za a bukaci a cike su bayan sauyin da aka samu
  • Idanu sun koma kan wadanda Tinubu zai zaba, ‘Yan APC da magoya baya sun sa ran samun mukamai

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya shirya cike guraben da sun zarce 2, 000 bayan ruguza shugabannin majalisun da ke kula da hukumomi 153 da aka yi.

Rahoton Punch ya bayyana cewa a sakamakon matakin da shugaban Najeriya ya dauka, za a bukaci akalla mutanen da za su canji wadanda aka tsige.

Shugabannin da aka sauke su na cikin wadanda Mai girma Muhammadu Buhari a Disamban 2017 bayan shekaru biyu da rabi da hawa kan mulki.

Kara karanta wannan

Ciki Ya Ɗuri Ruwa, DSS Sun Je Gidan Abdulrasheed Bawa, An Zurfafa Binciken EFCC

Bola Tinubu
Bola Tinubu a kasar Faransa Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Buhari ya rantsar da shugabannin wasu hukumomin ne daf da zai sauka, kafin su gyara zama har aka sauke su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kujeru masu tsoka a Gwamnati

Fitattun hukumomin da ake sauraron a ji shugabannin da za su rika sa masu ido su ne NEDC, ICPC, JAMB, TRCN, NSIT, NUC, da kamfanin TCN.

Sannan akwai NIMET, NCAT, NDIC, NIMC, WARC, NDDC da NBS. Saura hukumomin da aka samu gurabe a cikinsu sun kunshi FIRS da FAAN.

Akwai hukumar kwastam da ta kula da jin dadin ‘yan sanda da hukumar hana fataucin mutane. Hasashe ya bar guraben a kimanin 2, 000.

Lokacin sakayya ko duba cancanta?

Masu bibiyar sha’anin mulki su na ganin Bola Tinubu zai cika mukaman ne da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, ana tunanin su za su samu kujeru masu tsoka.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

Watakila nadin mukaman ya zama cikin sakayyar da shugaban kasa zai yi wa mutanensa, akwai magoya bayan da su ka taimaka masa a zabe.

Wasu da za ayi la’akari da su a nan su ne jagororin jam’iyyar APC mai mulki da kuma wadanda su ka yi takara a zaben da ya gabata, amma ba su dace ba.

A wasu hukumomin, zai yi kyau da shugaban Najeriya ya duba cancanta wajen bada mukaman. Jaridar ta ce daga ciki akwai TCN mai kula da lantarki.

Tinubu ya yi rushe-rushe

A makon nan rahoto ya zo cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sallami daukacin wadanda Muhammadu Buhari ya nada a lokacin ya na rike da mulki.

A doka akwai masu kula da duka ayyukan da ake yi a hukumomi da ma’aikatun gwamnati. Sai da majalisar shugabannin hukumomin ke aiki da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng