Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, Ya Ziyarci Shugaba Tinubu a Villa
- Sabon shugaban majalisar dattawa da ya karɓi rantsuwar kama aiki ranar Talata, Godswill Akpabio, ya ziyarci shugaban ƙasa a Villa
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da Sanata Akpabio, gwamnan jihar Imo, da Ganduje yanzu haka a fadarsa da ke Abuja
- Rahoto ya nuna cewa tun da safe, Tinubu ya gana da tsohon shugaban ƙasa Jonathan amma har yanzu ba'a faɗi abinda suka tattauna ba
FCT Abuja - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yanzu haka sabon shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya isa fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Akpabio ya kai ziyara ta musamman ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, jim kaɗan bayan ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban majalisar dattawa na 10.
Sanatan daga jihar Akwa Ibom karkashin inuwar APC ya samu nasara da kuri'u 63 a zaɓen da aka gudanar ranar Talata da safe, inda abokin karawarsa, Abdul'aziz Yari, ya samu kuri'u 46.
Tinubu ya shiga ganawa da Akpabio da wasu jiga-jigai a Villa
A halin yanzu, rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugaba Tinubu ya shiga ganawa da sabon zaɓaɓɓen shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a Aso Rock.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sauran waɗanda suka shiga wannan taro sun hada da gwamnan jihar Imo kuma shugaban kwamitin zaben majalisar dattawa na APC, Hope Uzodinma, wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.
Haka nan kuma rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, yanzu haka yana cikin fadar shugaban ƙasa.
Tinubu ya gana da Jonathan tun da safe
Tun da farko, shugaban ƙasa ya gana da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a ofishinsa da safiyar yau Talata, 13 ga watan Yuni.
Sai dai har yanzun babu cikaken bayani kan abinda suka tattauna. Ana tsammanin shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, zai gana da Tinubu.
Bayan Doke Yari, An Rantsar da Akpabio a Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa
A wani rahoton na daban kuma Sanata Akpabio ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa Na 10 a tarihi.
Sanatan, tsohon ministan Neja Delta ya kama aiki ne bayan doke babban abokin karawarsa, Abdul'aziz Yari daga jihar Zamfara ranar Talatan nan da muke ciki.
Asali: Legit.ng