Lagas, Ribas Da Wasu Jihohin Da Jam’iyyar Adawa Bata Taba Mulki a Cikinsu Ba
A duk shekarar zabe, jam'iyyun siyasa na fita don kwato sabbin jihohi da kuma jajircewa wajen ganin wuraren da suke mulki bai kubce masu ba.
Sai dai kuma, wasu jihohi takwas cikin 36 da ke Najeriya basu jijjiga ba tun 1999, domin dai har yanzu wata jam'iyyar adawa bata taba mulki a cikinsu ba.
Ga jerin jihohin da wata jam'iyyar adawa bata taba mulki a cikinsu ba tun 1999 a kasa:
Jihar Lagas
Tun bayan dawowar damokradiyya a 1999, lokacin da jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) ta lashe kujerar gwamna, jihar Lagas bata taba fadawa a hannun yan adawa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga AD zuwa jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) da All Progressive Congress (APC), jihar dai ta kasance ne a hannayen shugabanni guda.
AD ta koma ACN a Lagas bayan shugaban kasa Bola Tinubu, wanda ya kasance gwamnan jihar ya bar AD don kafa sabuwar jam’iyya. Jam’iyyar ACN ta yi maja da CPC, ANPP, da sauran jam’iyyun siyasa inda suka kafa APC.
Jihar Delta
Jihar ta kasance a hannun jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tun 1999. Jam'iyya mai mulki a jihar Delta ta kasance PDP.
Jihar ta kudu maso kudu ta yi gwamnoni hudu dukkansu daga jam'iyya daya.
Jihar Akwa Ibom
Wannan wata jaha ce ta kudu maso kudu da ta ki yarda ta watsar da babbar jam'iyyar adawar kasar, PDP, tsawon shekaru 24 da suka gabata.
Tun daga shekarar 1999 har zuwa 2023, jam'iyyar PDP ce ke rike da kambun shugabanci a jihar Akwa Ibom.
Jihar Ribas
Jihar Ribas na daya daga cikin jihohin da PDP ta yi zaman katutu a kan kujerar gwamna.
Tun 1999 sakamakon zaben guda daya ne inda jam'iyyar PDP ke yin nasara.
Jihar Bayelsa
Saura kadan jihar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta rasa matsayinta cikin jerin jihohin da jam'iyyar adawa bata taba mulki a cikinta ba lokacin da Gwamna mai ci Diri ya sha kaye a hannun dan takarar APC. David Lyon a zaben gwamna na Disambar 2019.
Sai dai kuma, nasarar APC ba ta kai ko'ina ba yayin da kotu ta tsige Lyon saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatarwa INEC da bayanan karya.
Jihar Enugu
Jihar Enugu ita ce ta gaba cikin rukunin jihohin da ba a taba samun dan adawa da ya yi shugabanci a cikinta ba. Ita kadai ce jihar kudu maso gabas da ke karkashin PDP kuma ta tsallake guguwar zaben Peter Obi wanda ya share yankin a zaben da ya gabata.
Jihar Borno
Mahaifar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ta ci gaba da bin tsarin zabe guda cikin shekaru 24 da suka gabata.
Da farko jam'iyyar All Peoples Party (APP) wacce ta rikide ta zama All Nigeria Peoples Party (ANPP) sannan ta koma APC ce ke shugabanci a jihar.
Jihar Yobe
Jihar Yobe ita ce ta karshe a wannan rukunin kuma tana kamanceceniya da makwabciyarta ta arewa maso gabas wato Borno.
Yobe tana da irin tsari guda da Borno, tun daga APP, ANPP, zuwa APC a 2015.
Zaman lafiyar Najeriya na gaba da aljihunmu, Shettima ga zababbun sanatoci
A wani labari na daban, Mataimakin shugaban kasa ya ja hankalin zababbun sanatoci gabannin rantsar da majalisa ta 10.
Kashim Shettima ya kalubalanci yan majalisar da kada su yarda su karbi cin hanci wajen zabar shugabanni.
Asali: Legit.ng