Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Watsi da Umarnin Gwamnan Filato, Ya Koma Aiki
- Ɗaya daga cikin Ciyamomi 17 da gwamnan Filato ya dakatar ya yi bore, ya koma Ofis ranar Jumu'a 9 ga watan Yuni
- Shugaban ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Usman Bala, ya ce gwamna bai da ikon dakatar da su daga muƙamansu
- A kwanakin baya majalisar dokoki ta shawarci gwamna Caleb Mutfwang, ya dakatar da Ciyamomin don yin bincike kuma ya hau ya zauna
Plateau - Dakataccen shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, Shehu Usman Bala, ya koma bakin aiki ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni, 2023.
Shugaban ƙaramar hukumar ya koma Ofis ya ci gaba da aiki duk da sabon gwamnan Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya dakatar da su daga aiki har sai an gama bincike.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi 17 biyo bayan shawarin da ya karba daga majalisar dokokin jihar Filato.
A cewar majalisar, ya kamata ciyamomin su bar Ofis domin a samu cikakkiyar damar gudanar da bincike kan tuhumar da ake masu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ciyaman ɗin Jos ta Arewa ya yi fatali da matakin dakatarwan
Honorabul Bala ya dira Ofishinsa da misalin ƙarfe 9:50 na safiyar ranar Jumu'a, inda ya bayyana cewa haka kurum gwamna ba shi da ikon dakatar da shi a dokance.
Ya ce yana nan daram a matsayin shugaban ƙaramar hukuma matuƙar ba wata Kotu wacce take da iko ta yanke hukunci saɓanin haka ba.
A kalamansa, ya ce:
"Ya zama dole a bi matakan doka, muna nan a matsayinmu na ciyamomi. Mutane sun bani amanar gwamnatin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa kuma na zo nan na ci gaba da kokarin sauke nauyin da aka ɗora mun."
"Kowa ya kwantar da hankalinsa kuma a bi doka sau da ƙafa, ina kira ga mai girma gwamna kar ya bari wasu maƙiya su hure masa kunne ya kauce wa hanya."
Tun bayan dakatar da su da kwana uku, Ciyaman din ya tara 'yan jarida ya shaida musu cewa gwamna ba shi da ikon ɗaukar wannan matakin a kansu, kuma suna nan a matsayin Ciyamomi a idon doka.
Gwamnan PDP ya fara soke tsarukan magabacinsa
A wani labarin na daban kuma Gwamnan jihar Filato ya dakatar da wasu ma'aikata daga bakin aiki.
A wata sanarwa da kakakin gwamna, Gyang Bere, ya fitar, ya ce gwamnan ya dakatar da ma'aikatan da aka ɗauka aiki tun 2022.
Asali: Legit.ng