Muhimman Abubuwa 5 Da Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Yi Domin Ceto Nijeriya Daga Halin Da Take Ciki
A yanzu dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban Najeriya wanda aka rantsar a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Ana masa kallon babban ginshiƙi ga yan siyasa da dama a Najeriya, wanda ya goya da dama daga cikinsu har suka zama abinda suka zama a yanzu.
Tinubu dai zai fuskanci ƙalubale da dama da suke yi wa ƙasar barazanar iya ci gaba da zama a yadda take.
Dole ne Tinubu ya yi ƙoƙarin samar da tsare-tsare masu kyawu domin magance matsalolin da ke addabar ƙasar na tsawon lokaci.
Ga muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya maida hankali akai:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Yaki da 'yan ta'adda ko 'yan fashin daji
Matsalar 'yan ta'adda ko 'yan fashin daji, ita ce matsala ta farko da a yanzu ta fi addabar Najeriya. Matsalar dai ta yi ƙamari ne a yankin Arewacin Najeriya.
Ku tuna cewa, gwamnatin Buhari da ta shuɗe, ta yi yaƙi da ‘yan Boko Haram kafin zuwan ‘yan ta'addan daji da dukkansu suka addabi yankin Arewacin Najeriya.
Akwai buƙatar Shugaba Tinubu ya yaƙi 'yan ta'addan daji da wuri, saboda irin yadda ayyukansu ke janyo asarar rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
2. Rage yawan ma'aikatu da wasu muƙaman gwamnati
Ana kashe kuɗaɗen Najeriya masu yawa wajen tafiyar da ma'aikatun gwamnati da dama da ya kamata a ce an haɗe su wuri ɗaya.
A baya-bayan nan dai an jiyo tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo (SAN) yana cewa, muƙamin ƙaramin ministan ya saɓawa tsarin mulkin Najeriya.
Akwai buƙatar Tinubu ya sa a rage yawan hadiman shugaban ƙasa, sannan a yi amfani da kuɗaɗen da za su yi rara domin ragewa talakawa wahalhalun da suke ciki.
3. Samar da mafita ga rikicin Kudu maso Gabas
Tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya wata babbar matsala ce ga sabon shugaban ƙasar.
Mutane da dama 'yan asalin yankin da ma waɗanda ba 'yan asalin yankin ba, sun rasa rayukansu a sanadin rikice-rikicen na 'yan a ware.
Fitattun mutane da dama, ciki harda sanannun 'yan siyasa sun rasa rayukansu a ayyukan 'yan tada ƙayar baya na yankin Kudu maso Gabas.
Mutane irinsu Chike Akunyili, mijin tsohuwar shugabar Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), Dora Akunyili, da Ahmed Gulak, jigo a jam'iyyar APC, na daga cikin irin mutanen da suka rasa rayukansu sanadin ayyukan 'yan a waren.
4. Gyara fannin kiwon lafiya da samar da ingantaccen yanayi ga likitoci
Akwai buƙatar gwamnatin Tinubu ta magance ƙalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiyar Najeriya.
Bangaren, kamar yadda yake a yanzu, yana buƙatar gyara ta yadda mutane za su rage fita ƙasar waje neman magani. Yana da kyau gwamnati ta samar da kayan aiki a asibitocin ƙasar da kuma ɗakunan gwaje-gwaje, musamman na manyan cututtuka.
Likitoci na yin ƙaura daga Najeriya zuwa ƙasashen waje galibi saboda rashin kyawun albashi, rashin gamsuwa da aikin, da kuma barazanar tsaro.
Don haka akwai buƙatar gwamnatin Tinubu ta magance wannan matsalar da ta ke barazana ga ɓangaren lafiyar ƙasar nan.
5. Sake tabbatar da ingancin tsarin zaɓe
Akwai buƙatar Tinubu ya mayar da hankali wajen magance duk wasu 'yan ƙananun matsaloli da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ke fuskanta a yayin gudanar da zaɓe.
Jinkirin da aka samu wajen shigar da sakamakon zaɓe a shafin duba zaɓe (IReV) ya janyo korafe-korafe a lokacin zaɓen da ya gabata.
Yayin da zaɓen gwamna a jihohin Imo da Kogi ke ƙaratowa, ana sa ran Tinubu zai yi wani abu cikin gaggawa domin dawo da ƙwarin gwuiwar da 'yan Najeriya ke da ita a kan INEC.
Kiristocin Najeriya sun faɗawa Tinubu abin da suke so
A wani labarin na daban, ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN), ta bayyanawa Shugaba Bola Tinubu abin da ta ke so ya yi wajen naɗe-naɗen muƙamai.
Ƙungiyar CAN ta ce idan ya tashi naɗa muƙaman hafsoshin sojojin Najeriya ya yi ƙoƙarin yin adalci ta hanyar tafiya da kowa da kowa.
Asali: Legit.ng