Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili

  • Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yada Labarai, Farfesa Dora Akunyili
  • Maharan sun far masa ne a yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba a jihar Anambra
  • Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da al'amarin

Wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yada Labarai, Farfesa Dora Akunyili.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kashe shi a Umuoji da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili
'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili
Asali: UGC

Kodayake har yanzu babu cikakken bayanai game da lamarin, wata majiya ta kusa da iyalan ta ce marigayin yana nan a taron kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Najeriya Nsukka (UNAA) inda aka karrama marigayiya Dora wasu sa’o’i kafin a kashe shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Majiyar, wacce kisan ya tarwatsa mata tunani, ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Allah, Ka mai da shaidan da mukarrabansa marasa karfi da rashin amfani.
“Na kasance tare da wannan mutumin jiya jiya a Sharon Hall, All Saints Cathedral, Onitsha. Ya kasance taron Kungiyar Tsofaffin Daliban Jami'ar Nsukka (UNAA), reshen Onitsha inda suka karrama marigayiya Dora Akunyili.
"Ya yi magana mai haske game da Dora kuma ya ba da gudummawar 500k ga ƙungiyar.
Ya kasance a wajen tare da dansa, Obum yanzu yana aiki tare da gwamnatin jihar Anambra.
“Mun raka su wajen motar kuma ya kasance abin tausayi lokacin da Obum ya rungume shi sosai yayin da su biyun suka rabu don shiga motocinsu mabanbanta.
“Obum yana cikin farin Hilux yayin da mutumin ke cikin babban Jeep (ina tsammanin Prado). Allah ya jiƙansa! ”

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A wani labari na daban, rundunar 'Yan sanda a jihar Kano ta dakile yunkurin sace mutane a kauyen Danzabuwa, da ke karamar hukumar Bichi.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce wannan ya biyo bayan korafin da wani mazaunin Kauyen Danzabuwa, Karamar Hukumar Bichi, Jihar Kano ya shigar, cewa an tuntube shi ta waya kuma an yi masa barazanar biyan Naira miliyan daya ko kuma a sace shi ko daya daga cikin ‘ya’yansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel