Buhari Ya Kashe Sama da Dala $19m da Dangote Ya Kashe Wajen Gyara Matatun Mai, Sule

Buhari Ya Kashe Sama da Dala $19m da Dangote Ya Kashe Wajen Gyara Matatun Mai, Sule

  • Gwamna Sule ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta kashe sama da kuɗin da Ɗangote ya kashe da nufin gyara matatun Najeriya
  • Ya ce har yau matatun ba su da amfani amma Ɗangote ya gina matatar da babu kamarta a Nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya
  • Gwamnan ya ɗora laifin karuwar kuɗin tallafin man da ake cece kuce bayan cirewa kan rashin aikin matatu 3

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, ta kashe sama da kuɗin da Ɗangote ya gina matatar mai a kokarin tashin matatun man Najeriya.

A lokuta daban-daban cikin shekaru 8 da Buhari ya shafe kan madafun iko, gwamnatinsa ta ba da kwangilar gyaran matatun mai da ke Kaduna, Patakwal da Warri, amma har yau babu mai rai.

Matatar Ɗangote.
Buhari Ya Kashe Sama da Dala $19m da Dangote Ya Kashe Wajen Gyara Matatun Mai, Sule Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A halin yanzu, da dala biliyan $19bn, Aliko Ɗangote, ya gina matatar man da babu kamarta a faɗin nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu, Sun Bayyana Matsayarsu Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur

Da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na kafar Channels tv, Gwamna Sule ya ce matatar Ɗangote zata canja wasan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdullahi Sule ya ce:

"Ku duba makudan kuɗin da gwamnatin Muhammadu Buhari, ta kashe da nufin gyara matatun man Najeriya. A shekaru 8, Buhari ya kashe kuɗi fiye da dala biliyan $19bn da Ɗangote ya kashe wajen gina Matatar mai."
"Matatu uku da muke da su a Najeriya suna iya tace gangar mai 450,000 ne a kowace rana amma matatar Ɗangote zata riƙa tace ganga 650,000 a duk rana."
"Ya kashe dala biliyan $19bn wajen ginata, mu kuma ba sabuwa muka gina ba, gyara waɗanda muke da su kaɗai y laƙume kuɗi sama da haka amma har yanzu basu aiki."

Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan kuɗin tallafin man fetur a aka cire, wanda ya haddasa cece-kuce a kasar nan, ya ɗora laifin ƙaruwar tallafin kan rashin aikin matatun.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

Yadda BVAS Ta Gaza Tura Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

A wani rahoton na daban kuma Ma'aikatan INEC sun ba da shaida a gaban Kotun zaɓe kan yadda BVAS ta gaza tura sakamakon zaben shugaban ƙasa.

Ma'aikatan INEC na wucin gadi sun bayyana cewa bisa tilas suka bi wata hanyar haɗa sakamakon bayan sun gano BVAS ba zata iya komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel