Shugabannin Majalisa: Tinubu Zai Yi Ganawar Karshe da Gwamnoni, Sanatoci da NWC

Shugabannin Majalisa: Tinubu Zai Yi Ganawar Karshe da Gwamnoni, Sanatoci da NWC

  • Bola Ahmed Tinubu ya karkata ga zaben shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da za ayi
  • Sabon shugaban kasar ya hadu da masu meman takarar shugaban majalisar wakilai, ya lallashe su
  • A yau Tinubu zai sa labule da Gwamnoni da shugabannin APC da kuma zababbun Sanatocin jam’iyyar

Abuja - Yayin da ake shirin rantsar da zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya da na dokoki, masu neman shugabanci sun yi nisa a shirye-shiryensu.

Ganin an kammala tattaunawa da ‘yan kwadago a kan batun cire tallafin fetur, The Nation ta ce hankalin Bola Ahmed Tinubu ya koma kan ‘yan majalisa.

Sabon shugaban kasar ya na so a samu shugabannin da zai ji dadin aiki da su a majalisa.

Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ana sa ran ba da dadewa ba, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi maganar shirin rantsar da sababbin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai a makon gobe.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Wa Lawan Da Gbajabiamila Sabon 'Aiki' Mai Muhimmanci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce a yau ne Shugaba Tinubu zai hadu da gwamnonin jihohin APC mai-mulki da kuma shugabannin jam’iyyar (NWC) kan batun zaben majalisar.

Za a hadu da Sanatoci

Bayan wannan taro da za ayi, a gobe Tinubu zai hadu da zababbun Sanatoci na APC.

Kafin nan, shugaban ya yi zama na musamman da zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya na APC da nufin kawai kai ya hadu wajen zaben shugabanninsu.

Haka zalika sabon shugaban na Najeriya ya sa labule da ‘yan majalisar da ke adawa da Tajudeen Abbas, su ka dage a kan cewa sai sun tsaya takara da za ayi.

An shawo kan 'Yan G7?

Da farko Tinubu ya fara yin zama ne da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Idris Wase.

Daga baya an rahoto cewa shugaban kasar ya yi kus-kus da Yusuf Gagdi (Pankshin/Kanke); Sada Soli (Jibiya /Kaita) da Miriam Onuoha (Okigwe ta Arewa).

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC Sun Fadi Waɗanda Suka Fi Cancanta da Shugabancin Majalisar Tarayya

Haka zalika ya zauna da Muktar Betara (Biu/Bayo/Shani/Kwayar Kusar) duk a yammacin Talata.

Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore ya halarci zaman da aka yi da ‘yan majalisar, kuma an jima kadan ake sa ran za a hadu da NWC.

Kamar yadda Tinubu ya roki Wase, Betare, Gagdi da sauransu su janyewa Abbas, zai nemi alfarmar nan wajen Sanatocin da ke adawa da Godswill Akpabio.

Wani Sanata wanda za ayi taron na yau da shi ya bayyana cewa ya zama dole Mai girma shugaban kasa ya tsoma baki kafin ranar da za a rantsar da su.

Tinubu ya hadu da 'Yan majalisa

A baya an ji labari cewa a farkon makon nan, Bola Tinubu zai sa labule da ‘Yan majalisa masu shiga ofis, hakan zai ba shi damar haduwa da ‘yan adawa.

Sanarwar da aka aikawa Sanatoci da ‘Yan majalisar sun nuna da karfe 3:00 na Litinin za a fara taron a Aso Rock, ba mu san yadda zaman na su ya kare ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel