Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa
Nasarar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu zuwa lokacin da ya zama shugaban ƙasa ta gamu da matsaloli da ƙalubale iri-iri.
Akan hanyarsa ta zama shugaban ƙasar Najeriya, Tinubu ya fuskanci ƙalubale da dama a ciki da wajen jam'iyyarsa ta APC.
Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin manyan ƙalubalen da shugaba Tinubun ya tsallake masu matuƙar haɗari kafin zamansa shugaban ƙasar Najeriya.
1. Buhari baya son Tinubu
Abu na farko cikin ƙalubalen da Tinubu ya tsallake shi ne labarin da aka yi ta yaɗawa, na cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya sonsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kafin zaben fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, an ce Buhari bai so Tinubu ya yi nasara ba. Sai dai tsohon shugaban ya musanta zargin 'yan kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
2. Batun Ahmad Lawan
Ana tsaka da batun zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a tsakiyar shekarar 2022, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa, Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa, shi ne dan takarar da jam’iyya mai mulki da Buhari suka amince da shi.
An ce sanarwar dai an yi ta ne da nufin karkatar da hankulan jama’a daga harkokin zaɓen da ke gudana a lokacin, amma duk da haka Tinubu ya samu nasarar tsallake tuggun, inda a karshe ya lashe zaben shugaban kasar na 2023.
3. Arewa za ta munafurci Tinubu
Wani ƙarin abin da ya nemi ya kawowa Tinubu cikas kan hanyarsa ta zama shugaban ƙasa shi ne, iƙirarin da wasu suka yi, na cewa Arewa musamman ma gwamnonin Arewa, za su ci amanar Tinubu kamar yadda suka yi wa Marigayi Cif MKO Abiola.
Ɗaya daga cikin fitattun ‘yan adawa Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Afenifere, ne gaba-gaba wajen bayyana wannan batu. Sai dai Adebanjo daga baya ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga Peter Obi na jam’iyyar Labour.
4. Osinbajo babbar barazana ne
Daga cikin labaran da aka riƙa yaɗa cewa za su kawowa Tinubu cikas wajen zamansa shugaban ƙasa shi ne, iƙirarin cewa ba zai iya kayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo a zaben fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ba.
Tinubu dai shi ne tsohon ubangidan Osinbajo kuma shi ne ya turo shi a matsayin abokin takarar Buhari a zaɓen 2015.
5. Tinubu ya zagi Buhari a Abeokuta
Kalaman Tinubu a Abeokuta cikin fushi, inda ya bayyana yadda ya gamsar da tsohon shugaban ƙasa Buhari kan tsayawarsa takara a zaɓen 2023, na daga cikin abubuwan da ake ganin zasu jawo masa faɗuwa zaɓe a lokacin.
Amma duk a cikin hakan, sai da shugaba Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
6. Dubunnan wasiku zuwa Jami'ar Chicago
Gabanin zaɓen 2023, an yi ta cece-kuce a kan batun karatun shugaba Tinubu da ya ce ya yi a jami'a.
Saboda yadda jam’iyyun adawa suka zaƙu, an rubuta wasiku da dama zuwa jami’ar Chicago, makarantar da Tinubu ya bayyana cewa can ya kammala karatunsa.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Reno Omokri, jigo a jam'iyyar PDP, ya bayyana martanin da ya samu daga jami'ar a lokacin da ya tuntuɓesu kan batun na Tinubu.
7. Karancin man fetur
Kimanin wata guda ya rage a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, an samu ƙarancin man fetur a ƙasa baki ɗaya, matakin da ake zargin wasu jam’iyyun adawa da goyon bayan wasu manya a Aso Rock da shiryawa domin daƙile nasarar Tinubu.
Tinubu ya yi tsokaci kan hakan a lokacin da ya je yaƙin neman zaɓe a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, gabanin babban zaɓe.
8. Sauya fasalin Naira
Sauya fasalin kuɗi da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi, na daga cikin manyan abubuwan da suka girgiza al’ummar ƙasa gabanin zaɓen da Tinubu ya yi nasarar lashewa.
Haka zalika, Tinubu da wasu gwamnonin jam’iyyar APC, sun bayyana cewa an kawo tsarin sauya fasalin kuɗin ne domin a yaƙi takarar da Tinubu yake yi a lokacin.
9. Haduwar Obi da Kwankwaso
Daga cikin barazanar da Tinubu ya fuskanta a yayin neman zama shugaban Najeriya shi ne, batun haɗewar da akai zargin Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, da Peter Obi na jam’iyyar Labour da yi.
Sai dai daga ƙarshe, Kwankwaso da Peter Obi sun fito sun yi bayani gabanin zaɓe, inda suka bayyana cewa babu batun hadewar.
10. Ba za a rantsar da Tinubu ba
Bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe, wasu da dama daga ɓangaren ‘yan adawa sun yi iƙirarin cewa ba za a rantsar da Tinubu ba saboda a cewarsu, ya gaza samun kashi 25% na ƙuri'un da aka kaɗa a babban birnin tarayya Abuja lokacin zaɓe.
Har ila yau, da yawa daga cikin shugabannin Kiristoci, sun yi hasashe-hasashe daban-daban kan cewa tsohon gwamnan jihar Legas, sai dai ya hangi kujerar shugaban ƙasa, amma ba zai kai gareta ba.
Cire tallafin man fetur zai ɓata wa Tinubu gwamnati, Mallamin Addini
A wani labarin da muka wallafa a baya, kun ji shugaban wata babbar majami'a, Primate Elijah Ayodele ya fito yana nuna rashin goyon bayansa kan cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi.
Babban malamin majami'ar ya ce, cire tallafin na man fetur da Tinubu ya yi a yanzu zai iya ɓata masa gwamnatinsa, saboda a cewarsa, hakan ya yi wuri da yawa.
Asali: Legit.ng