Tsofaffin Gwamnonin Najeriya 5 Da Suka Fuskanci Ƙalubale Mako Guda Bayan Sun Bar Ofis
Kwanaki kaɗan bayan rantsar da sabbin gwamnoni da waɗanda suka dawo karo na biyu su 28 a shiyyoyin ƙasar nan shida, an fara samun takun saƙa tsakanin sababbi da tsofaffin gwamnonin.
Hakan na da alaƙa da irin yadda wasu daga cikin sababbin gwamnonin ke ganin an yi amfani da dukiya da kadarorin jiha ta hanyoyin da ba su dace.
Legit.ng ta zaƙulo muku wasu guda biyar daga cikin tsofaffin gwamnonin da a yanzu hake ke fuskantar ƙalubale daga magadansu a jihohinsu.
Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje na ɗaya daga cikin gwamnonin da suke fuskantar ƙalubale daga sabbin gwamnonin jihohinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A daren ranar Juma'a, wayewar garin Asabar ne sabon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da fara rushe gine-gine da ya ce an yi su ne a filayen gwamnati ba bisa ka'ida ba, kamar yadda ya zo a rahoton Daily Trust.
Abban ya fara ne da rushe wasu gine-gine a Filin Sukuwa, da kuma wasu wurare daban a cikin Kano, babban birnin jihar waɗanda tsohon Gwamna, Abdullahi Ganduje ya amince da su.
Tun ranar da aka rantsar da shi, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin tuhumar Ganduje kan kadin wasu maƙudan kuɗaɗen jihar har N241bn da aka bar masa bashi.
Bello Matawalle na Jihar Zamfara
A jihar Zamfara ma, tsohon gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ma na fuskantar barazana daga sabon gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare kan zargin badaƙalar kuɗaɗe.
Dauda Lawal ya bai wa Matawalle wa'adi kan ya maido duka motoci na alfarma da ya ce ya siya kan kuɗi N2,794,337,500 daga asusun gwamnatin jihar.
Dauda ya ce sun riga da sun bai wa tsohon gwamnan wa'adin kwanaki 5 da shi da mataimakinsa kan su yi gaggawar maido da waɗannan motoci da aka siya da kuɗin gwamnatin jihar.
Okezie Ikpeazu na Jihar Abia
Tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Victor Ikpeazu na ɗaya daga jerin gwamnonin da ke fuskantar ƙalubale bayan barinsu Ofis daga hannun sabbin gwamnonin jihohinsu.
Alex Otti, sabon gwamnan jihar ta Abia, ya bayar da umarnin rufe dukkanin asusun ajiyar kuɗaɗe na gwamnatin jihar da na hukumominta da ke a kowane banki da cibiyoyin hada-hadar kuɗi a fadin ƙasar nan.
Otti ya kuma rushe dukkannin wasu muƙamai na wasu hukumomi da gwamnatin jihar Abia ta baya ta ba da.
Otti ya kuma ce, sabon gidan gwamnati da magabacinsa Ikpeazu ya ƙaddamar, ba a kammala aikinsa ba, saboda haka zai binciki ingancinsa da kuma duba yadda za a ƙarisa aikin nasa.
Simong Lalong na Jihar Filato
Simon Bako Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato ma na fuskantar ƙalubale daga magajinsa Caleb Mutfwang.
A cikin makon da ya gabata ne sabon gwamnan na Filato ya fitar da wata sanarwa ta dakatar da duka shugabannin ƙanan hukumomi 17 na jihar.
Gwamnan ya ce matakin na zuwa ne saboda bincike da sabuwar gwamnatin jihar ke yi kan kadarorin ƙananan hukumomin da ma na jihar baki ɗaya.
Samuel Ortom na Jihar Benue
Tsohon gwamnan Benuwai na cikin fargaba, biyo bayan umarnin da sabon gwamnan jihar Hycinth Alia, ya bayar na rushe shugabannin hukumomin jihar tare da korar shugabanninsu.
Ya kuma umurci korarrun shugabannin da su miƙa dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga manyan jami’an ma’aikatunsu.
Gwamnonin Najeriya sun ziyarci Buhari a gidansa da ke Daura
A wani labarin da muka wallafa a baya, mun kawo muku cewa zaɓaɓɓun gwamnonin APC tare da wasu daga cikin na jam'iyyun adawa sun kai ziyara ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.
Tsohon mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Bola Tinubu: Abubuwa 2 Da Ke Faruwa a Kasa Wadanda Tinubu Bai Yi Magana a Kansu Ba Ranar Da Aka Rantsar Da Shi
Asali: Legit.ng