Jita-Jita: Shin Tinubu Ya Nada Pat Utomi, Aminin Peter Obi Minista? Jigon Jam'iyyar Labour Ya Mai da Martani
- Farfesa Pat Utomi ya musanta rahoton da ake yadawa cewa an nada shi mukami a sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tnubu
- Utomi ya bayyana haka ne ta bakin mai ba shi shawara a harkar yada labarai, inda ya bukaci mutane su yi watsi da wannan rahoto
- Ya ce a matsayinsa na mai goyon bayan jam’iyyar Labour da Peter Obi, karban mukami daga Bola Tinubu cin amana ne
FCT, Abuja – Farfesa Pat Utomi, dan siyasa kuma aminin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya barranta kansa da rahoton da ke yawo cewa an nada shi a matsayin minista a gwamnatin Tinubu.
Utomi ya bayyana haka ne ta bakin mai bashi shawara a kan yada labarai, Charles Odibo a wata sanarwa inda ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahoton.
Sahara Reporters ta tattaro cewa Utomi ya bayyana wannan shi ne karo na biyu da suke kokarin hakan don danganta shi da sabuwar gwamnati.
Utomi ya ce karban mukami cin amana ne
Pat Utomi ya ce karban wani mukami a gwamnatin Tinubu a matsayinsa magoyin bayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour kuma jigo a jam'iyyar, hakan cin amanar 'yan jam'iyarsu ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar da Vanguard ta samo ta ce:
“Wani rahoto ya ja hankalin Pat Utomi inda aka fitar da jerin wadanda za a bai wa mukamai a gwanatin Tinubu, yayin da aka bayyana Utomi a matsayin minista.
“Muna da kyakkyawan alaka da Utomi wanda ya kasance a kasar waje na tsawon wata biyu, inda ya bayyana cewa bai yi wata ganawa ba dangane da mukamin da aka ce an bashi ba.
“Ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wannan rahoton karya da ya ke danganta shi da sabuwar gwamnatin Shugaba Tinubu.”
An dade ana rade-radin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai iya bai wa Farfesa Pat Utomi matsayi a gwamnatinsa.
Bayanai Sun Bayyana Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Nasara, Inji ‘Dan Takaran LP
A wani labarin, dan takarar gwamna a jam'iyyar Labour a jihar Oyo, Tawfiq Akinwale ya bayyana yadda Tinubu ya yi amfani da jam'iyyarsu don cimma burinsa.
Tawfiq ya ce Shugaba Tinubu ya roki Pat Utomi da ya hakura da takarar shugaban kasa don samun biyan bukatar kansa.
Asali: Legit.ng