Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamna AbdulRazak da Gwamna Uzodinma Murna
- Shugaba Tinubu ya taya sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, murna
- Bayan nan shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya taya sabon shugaban gwamnonin ci gaba na jam'iyyar APC (PGF)
- Ya ce shugabanci a matakin jiha yana da matukar amfani wajen nasarar kowace irin gwamnati
Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da sakon taya murna ga gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, bisa nasarar zama shugaban ƙungiyar gwamnoni (NGF).
Haka nan kuma shugaban ƙasan ya taya gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo murnar zama shugaban ƙungiyar gwamnonin ci gaba na APC, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar ranar Alhamis. Tinubu ya kuma taya mataimakansu gwamnoni 2 murna.
A kalamansa, shugaba Tinubu ya ce
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina taya gwamnan jihar Kwara, mai girma Abdulrahman Abdulrazaq, murnar zama shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) da gwamna Hope Uzodinma wanda ya samu nasarar zama shugaban ƙungiyar gwamnonin APC."
"Haka zalika ina taya mai girma Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo da takwaransa na Kaduna, Mallam Uba Sani, murnar zama mataimaka a ƙungiyoyin bi da bi."
"Zakulo ku da abokan aikinku suka yi domin ku shugabance su, babbar alama ce ta yarda da tsagwaron aminta da gwamnonin suka yi muku."
Sabon shugaban ƙasan ya kuma buƙaci sabbin shugabannin da su yi amfani da wannan dama da Allah ya basu a zangon mulki ɗaya wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban kasa.
Bugu da ƙari ya yi kira da su haɗa karfi da karfe tare da gwamnatinsa domin tabbatar da kudirin sabunta fata nagari a zuƙatan al'umma.
Ya ce a matsayinku da shugabanni a jihohi kuna da matuƙar muhimmanci wajen nasarar wannan sabuwar gwamnatin.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a Villa
A wani labarin na daban kuma Shugaban ƙasa ya gana da yan takarar kujerar kakakin majalisar wakilan tarayya da mataimaki a fadarsa da ke Abuja.
Da yake jawabi ga yan jarida bayan ganawa da shugaba Tinubu, Abbas ya ce ranar 13 ga watan Yuni zai zama shugaban majalisar wakilan tarayya yayin da Kalu zai zama mataimakinsa.
Asali: Legit.ng