Shugaba Tinubu Ya Gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a Villa

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a Villa

  • Shugaban ƙasa ya gana da yan takarar kujerar kakakin majalisar wakilan tarayya da mataimaki a fadarsa da ke Abuja
  • Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu sun ziyarci Bola Tinubu ne domin taya shi murna bayan rantsar da shi ranar Litinin
  • Abbas ya ce idan Allah ya amince zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2023 ya zama kakakin majalisar tarayya ta 10

Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Honorabul Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a fadarsa Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis.

Idan baku manta ba Abbas da Kalu sun samu cikakken goyon bayan jam'iyyar APC a takarar kakaki da mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya ta 10.

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a Villa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Leadership ta rahoto cewa wannan goyon bayan na APC ya gamu da tasgaro daga wasu mambobin majalisar kuma 'ya'yan jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki, Bayanai Sun Fito

Me suka tattauna a taron?

Wannan ganawa na zuwa ne yayin da ake tunkarar ranar rantsar da mambobin majalisar wakilan tarayya ta 10 wanda aka tsara gudanarwa ranar 13 ga watan Yuni, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi ga yan jarida bayan ganawa da shugaba Tinubu, Abbas ya ce ranar 13 ga watan Yuni zai zama shugaban majalisar wakilan tarayya yayin da Kalu zai zama mataimakinsa.

Ya ce sun gana da shugaban ƙasa ne domin taya shi murna bisa nasarar da ya samu a babban zaɓen 2023 da kuma rastuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Ya kuma yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa cewa majalisa ta 10 zata zama 'yar amshin shata, inda ya karfafa cewa babu wanda ya isa ya tilastawa Mambobi 360 amince wa da abinda ba zai zame wa kasar nan alheri ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Jihar Arewa Ta Dakatar da Ciyamomi Da Kansiloli a Kananan Hukumomi 17

Vanguard ta rahoto shi yana cewa:

"Ni ne Tajudeen Abbas, ɗan majalisar tarayya kuma a tare dani abokin aiki ne wanda in sha Allah zuwa ranar 13 ga watan Yuni, mun zama kakaki da mataimkinsa a majalisa ta 10."
"Idan baku manta ba kwana 2 zuwa 3 da suka shige shugaban kasa ya karbi mulki, tun wannan lokacin bamu gana da shi ba, shiyasa muka ga ya dace a matsayin yan takarar jam'iyya, mu zo mu taya shi murna."

EFCC Ta Titsiye Tsohon Gwamnan APC Da Ya Sauka Kan Zargin Wawure Biliyan N4bn

A wani labarin kuma Jami'an hukumar EFCC sun tasa tsohon gwamnan APC da tambayoyi bisa zargin sauya wa wasu kuɗaɗen haram akala.

Rahoto ya nuna tsohon gwamnan na APC, Kayode Fayemi, ya isa ofishin EFCC na Ilorin, jihar Kwara da karfe 9:40 na safiyar Alhamis

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel