Yanzu Yanzu: Tinubu Na Ganawa da Oshiomhole, Kungiyoyin NLC da TUC

Yanzu Yanzu: Tinubu Na Ganawa da Oshiomhole, Kungiyoyin NLC da TUC

  • Wakilan gwamnatin tarayya na cikin ganawa da shugabannin kungiyoyin NLC da TUC kan cire tallafin man fetur
  • Ganawar tasu na zuwa ne awanni bayan kamfanin NNPCL ya sanar da sabon farashin man fetur a fadin gidajen manta da ke kasar
  • Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya halarci ganawar wanda shugabannin NLC da TUC suka jagoranta

Shugabancin kungiyar kwadago ta kasa na cikin wata ganawa da gwamnatin tarayyar Najeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kungiyar kwadagon ta samu jagorancin shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamrad Joe Ajaero da takwaransa na kungiyar kasuwanci ta TUC, Kwamrad Festus Osifo.

Adams Oshiomhole da shugaban kasa Bola Tinubu
Yanzu Yanzu: Tinubu Na Ganawa da Oshiomhole, Kungiyoyin NLC da TUC Hoto: Adams Oshiomhole, Buhari Sallau
Asali: Facebook

Taron na gudana ne a dakin taro na shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Daily Trust ta rahoto.

Wadanda suka halarci ganawar da ke gudana a Aso Rock

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Zabi Gwamna Uzodimma a Matsayin Shugaban Gwamnonin APC, Cikakken Bayani Ya Bayyana

Cikin wadanda suka hallara akwai tsohon shugaban NLC kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamrad Adams Oshiomhole, sakataren dindin na fadar gwamnati, Tijjani Umar, shugabar ma'aikatan tarayya, Dr. Foldable Yemi-Esan, shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana gudanar da taron ne bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewar an cire tallafin man fetur sannan NNPCL ta sanar da sabon farashin mai, rahoton Punch.

Kungiyar NLC ta yi watsi da sabon farashin man fetur

Mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa ta yi watsi da sabon farashin da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, kamfanin man fetur din ya ba gidajensa a fadin kasar umurnin siyar da fetur tsakanin N480 da N570.

Da yake martani ga ci gaban, shugaban kungiyar NLC, Kwamrad Joe Ajaero, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Labour House, Abuja a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, ya ce kungiyar ba za ta lamunci hakan ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Sabon Gwamnan Taraba Ya Rantsar Da SSG Da Shugaban Ma’aikata

Binciken Gaskiya: Tinubu Bai Sanar Da Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa Ba

A wani labarin kuma, bincike ya nuna cewahotuna da dama da masu amfani da dandalin WhatApp suka daura a shafukansu na ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin rage alawus din da ake ba yan bautar kasa (NYSC) ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel