Gwamna Ya Rantsar da Wasu Kwamishinoninsa Kwanaki 2 da Hawa Karagar Mulki
- Siminalayi Fubara ya zabi wasu Kwamishinoni, kuma har ya rantsar da su domin su fara aiki
- Sabon Gwamnan na jihar Ribas bai bata lokaci ba, ya fara nada wadanda zai yi aiki da su a mulkinsa
- A ranar Litinin aka rantsar da Fubara a Fatakwal bayan wa’adin Gwamna Nyesom Wike ya kare
Rivers - Mai girma Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya rantsar da Kwamishinoni hudu, hakan na zuwa ne kwanaki kadan da shiga ofis.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya nada Kwamishinoni hudu, ya na mai kira a gare su da su yi aiki da zai nuna irin kishinsu.
Kwamishinonin da aka zaba kuma aka rantsar su ne: Farfesa Zacheous Adango, Dr. Alabo George Kelly, Farfesa Chinedu Mmom sai Barr Isaac Kamalu.
Kwamishinonin Wike sun dawo
Farfesa Adango da Mmom za su rike ma’aikatun shari’a da na ilmi, Barista Kamalu zai kula da harkar kudi, Dr. Kelly zai sake komawa ma’aikatar ayyuka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yammacin Larabar nan Mai girma Gwamna ya rantsar da su a gidan gwamnati da ke Fatakwal. Dukkansu hudu sun yi aiki a gwamnatin Nyesom Wike.
Tun a ranar Talata, Gwamna Fubara ya tura sunayen wadannan kwamishinoni zuwa majalisar dokokin Ribas domin a tantance kuma a tabbatar da su.
An rantsar da Dr. George Nweke
Baya ga Kwamishinonin, an rantsar da sabon shugaban ma’aikatan jiha, Dr George Nweke wanda Gwamnan Ribas ya ce an zabo shi ne bisa cancantarsa.
Haka zalika Ibierembo Thompson ya samu shiga cikin hukumar zabe ta jiha watau RSIEC.
Channels TV ta ce Fubara ya nuna akwai aiki a gaban gwamnatinsa, don haka ya kamata ayi gaggawar daura ginin da zai zama tubalin shekaru hudu.
Fubara wanda aka rantsar a matsayin Gwamna a makon nan yake cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin an kama hanyar da za a kawo gyara a Ribas.
Akwai buri a kan gwamnati
A cewar Fubara, mutanen Ribas su na da buri sosai a kan gwamnatinsa, don haka sai an dage.
Sabon Gwamnan ya taya wadanda ya zama murna, ya yi kira a gare su da su yi amfani da gogewarsu a ofis wajen jagorantar ma’aikatarsu.
A jawabinsa, Gwamnan ya gargadi mutanen Ribas da cewa ka da a kawo masa wargi, ya ja-kunnen masu neman raina shi saboda irin saukin kansa.
Jawabin Remi Tinubu a coci
A baya an samu rahoto cewa Remi Tinubu ta tabo batun mulkin Najeriya a karkashin mai gidanta da ya gaji Muhammadu Buhari a farkon makon nan.
Sanatar Legas ta tsakiya ta ce watakila za ta zama Uwargidar Najeriya mafi tsufa da aka yi a tarihi, ta na mai rokon mutane su yi wa mai gidata addu'a.
Asali: Legit.ng