Jerin Sunayen Matasa 4 Da Buhari Ya Naɗa Da Ake Tunanin Tinubu Zai Cigaba Da Aiki Da Su

Jerin Sunayen Matasa 4 Da Buhari Ya Naɗa Da Ake Tunanin Tinubu Zai Cigaba Da Aiki Da Su

Daya daga cikin taken yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu mafi shahara akwai batun sanya matasa cikin harkokin mulki.

Ba za a iya misalta irin muhimmancin shigar matasa cikin harkokin mulki ba, kuma wannan batu ne da tuni ake ta ƙara samun ci-gaba a kansa a Najeriya.

Bisa la'akari da irin kaifin tunani, sabbin dabaru da kuma zumma da jini a jika, matasa za su iya kawo sauyi domin amfanin goben ƙasashensu.

Matasa da ake ganin Tinubu zai ci-gaba da tafiya da su
Sunayen matasa 4 masu mukami da ake ganin Tinubu zai ci-gaba da tafiya da su. Hoto: Asiwau Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A Najeriya an sami matasa da dama da aka naɗa muƙaman gwamnati, kuma an ga irin yadda suka yi aiki tuƙuru don ganin an samu ci-gaba da kuma zaburar da takwarorinsu.

Zuwan gwamnatin Tinubu, ta sanya mutane da dama fara hasaso matasa masu muƙamai, da ake ganin za su iya taka muhimmiyar rawa a cikin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ministocinsa, Da Masu Muƙami Suka Ji Tsoron Buhari a 2015

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu daga cikinsu da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta naɗa, sun nuna ƙwarewa, ƙwazo da kuma jajircewa da ake ganin za ta iya jan hankalin shugaba Tinubu ya tafi da su.

Legit.ng ta zaƙulo muku wasu fitattun matasa guda huɗu da suka taka rawar gani a gwamnatin Buhari, waɗanda kuma ake ganin za su iya ci-gaba da riƙe mukamansu a gwamnatin shugaba Tinubu.

1. Ahmad Salihijo Ahmad

An bai wa Ahmad Salihijo Ahmad a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, matsayin shugaban hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara (REA).

A karkashin jagorancin Injiniya Ahmad, REA ita ce ke aikin samar da wutar lantarki a Najeriya ta hanyar tallafin kuɗaɗe da hukumar ke samu daga bankin duniya da kuma bankin raya yankin Afirka (AfDB).

A karkashin shirin, ana ci gaba da yin ayyukan samar da wuta a shiyyoyi shida na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

A Ranar Farko, Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Mai Kyau Kan Sauya Takardun Naira

Ya zuwa yanzu, hukumar ta kammala kashi na farko na aikin, wanda a ƙarƙashinsa aka samar da matsakaitan tashoshi 12 na sola masu ɗauke da sama da na’urorin zuƙo hasken rana 19,000.

Dangane da kashi na biyu, ayyuka na ci-gaba da gudana don samar da ƙarin matsakaitan tashoshi 51 na sola.

2. Kashifu Inuwa Abdullahi, Diraktan NITDA

Kashifu Inuwa Abdullahi na ɗaya daga cikin waɗanda tsohon shugaban ƙasa Buhari ya naɗa waɗanda gwamnatin shugaba Bola Tinubu zata iya ci-gaba da tafiya da su.

Shi ne shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta ƙasa (NITDA), wanda aka naɗa a lokacin Buhari.

Kashifu ƙwararre ne kuma mai hangen nesa ne da ya ba da gudummawa sosai wajen ciyar da fasaha da kirkire-kirkire gaba a Najeriya.

Ya jagoranci tsare-tsare da dama da suka yi tasiri sosai kan sauye-sauyen da aka samu a fasahohin zamani ta fuskar inganci, karɓuwa a cikin gida da sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 Da Ke Ta Hankoron Kaddamar Da Ayyuka Gabanin Mika Mulki Gabanin Ranar 29 Ga Watan Mayu

Sauran sun haɗa da samar da ilimin tsaro na yanar gizo, kariyar bayanai, samun haɗin gwiwa da kamfanonin ƙasashen waje da dama.

3. Mista Modibbo R. Hamman Tukur

An naɗa Modibbo Ribadu Hamman Tukur a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a matsayin shugaban sashin kula da harkokin kuɗi na Najeriya (NFIU).

Tukur ƙwararre ne kan musayar bayanan sirri na ƙasashen waje, dawo da kadara da kuma huldar ƙasa da ƙasa, wanda ya shafe shekaru sama da 20 yana aiki a ɓangaren.

Ya kasance ƙwararre tun a lokacin da ya yi aiki da hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), inda ya riƙe muƙamin shugaban harkokin ƙasa da ƙasa.

4. Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC

Abdulrasheed Bawa, a yanzu haka shi ne shugaban hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC).

Tun da ya hau kan muƙaminsa a watan Fabrairun shekarar 2021, haziƙin mai yaƙi da cin hanci da rashawan ya yi suna sosai bisa ga tarin nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Abun Ba Daɗi: Yadda Masu Kwacen Waya Suka Kashe Mutane da Yawa a Cikin Birnin Kano

Kaifin basirarsa ya taimaka masa wajen samun alaƙa da hukumomin ƙasa da ƙasa irin su cibiyar bincike ta tarayyar Amurka (FBI), hukumar kula da laifukan ƙasa ta Burtaniya (NCA), da 'yan sandan ƙasa da ƙasa domin musayar bayanai.

Sauran abubuwan da aka danganta ga Abdulrasheed Bawa sun haɗa da dawo da kadarorin da aka sata, kyakkyawar hulɗar yaɗa labarai, dabarun yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma jin daɗin ma’aikatan da ke tare da shi.

Tinubu da Emefiele sun yi zaman gaggawa a fadar shugaban ƙasa

A wani labarin kuma, a yau Talata, 30 ga watan Mayu ne sabon shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya yi wani zama na gaggawa da shugaban babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, da kuma shugaban NNPC, Mele Kyari.

Ana ganin zaman na da alaƙa da batun sauya fasalin kuɗaɗe da Tinubun ya ce zai sake dubawa domin farfaɗo da darajar kuɗaɗen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel