Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis
- A safiyar 29 ga watan Mayun 2023, Najeriya za ta samu sabon shugaban kasa bayan shekaru takwas
- Tun daga gobe mutane za su fara bude kunnuwa domin jin mukaman da Bola Ahmed Tinubu zai raba
- Ana sa ran zababben shugaban Najeriyan ya fara nada kakaki, shugaban ma’aikatan fada da SGF
Abuja - A bisa al’ada, mutane su na tsammanin Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wasu daga cikin mukarraban Gwamnatinsa tun a ranar farko a mulki.
Akwai yiwuwar jim kadan bayan Olukayode Ariwoola ya rantsar da zababben shugaban kasar, ya sanar da manyan hadiman da za su aiki a kusa da shi.
Vanguard ta ce mukaman da shugabanni su ke fara nadawa su ne; Mai magana da yawun baki, Shugaban ma’aikatan fada sai sakataren gwamnati.
1. Mai magana da yawun baki
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Masu mulki su kan nada mai(su) magana da yawunsu ko sakataren yada labarai wadanda daga baya duk wata sanarwa daga ofishinsu za ta rika fitowa.
Ana ware wannan kujera ne ga kwararren ‘dan jarida, edita ko masanin hulda da jama’a.
Rahotan ya ce ana kawo sunayen ‘yan jarida da su ka yi aiki da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC irinsu Bayo Onanuga da Dele Alake.
Haka zalika tun yanzu akwai irinsu Abdulaziz Abdulaziz da Mahmud Jega wanda kwararrun ‘yan jarida ne da su ke aiki da ofishin zababben shugaban kasar.
2. Shugaban ma’aikatan fada
Wata muhimiyyar kujera yanzu a salon mulkin Najeriya ita ce ta shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, wanda kowa zai ga wa zai hau kan ta a gobe.
Wasu su na cewa wanda zai samu kujerar nan ya na tsakanin shugaban majalisar wakilai watau Femi Gbajabiamila, James Faleke da kuma Babatunde Fashola.
Duk wanda ya samu wannan kujera zai zama ya na da iko da fadar shugaban kasa, sai an fara kai wa gare shi sannan mutum zai iya yin ido biyu da Bola Tinubu.
3. Sakataren Gwamnati
Ba abin mamaki ba ne tun a wajen rantsuwa ko jim kadan bayan nan a ji Tinubu ya sanar da wanda zai zama sabon gwamnatin tarayya, zai gaji Boss Mustapha.
Ministoci da tsare-tsaren gwamnatin Najeriya su na karkashin Sakataren gwamnatin tarayya. A kan zabi kwararren ma’aikacin gwamati ko tsohon Minista.
Nasir El-Rufai, Aminu Masari da Atiku Bagudu su na cikin sunayen da ake yawo da su. Babu wanda zai iya cewa ga wanda sabon shugaban kasar zai dauko.
Sai an yi hakuri da farko
A ranar Juma'a aka samu labari cewa Kashim Shettima ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya, ya ce gwamnatinsu za ta fara da gargada a ofis saboda halin da ake ciki.
Zababben mataimakin shugaban kasar, Sanata Shettima ya na so jama’a su rage dogon buri a kansu, ya yi alkawarin fwamnatinsu za tayi wa kowa adalci.
Asali: Legit.ng