Kwankwaso Ga Yan Siyasa: Ku Daina Satar Kuɗin Talakawa, Ku Rika Gina Al'umma

Kwankwaso Ga Yan Siyasa: Ku Daina Satar Kuɗin Talakawa, Ku Rika Gina Al'umma

  • Rabiu Kwankwaso ya halarci taron lakcar da aka shirya a wani ɓangaren bikin rantsar da zababben gwamnan jihar Neja na APC
  • A jawabinsa, an ji Kwankwaso na rokon yan siyasa su maida hankali wajen gina jama'a maimakon wawure kuɗin gwamnati
  • A cewarsa gwamnoni da dama sun gaza a jihohinsu sakamakon rashin gogewa da ingantaccen ilimin shugabanci

Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP a zaben 2023 da ya wuce, Rabiu Musa Kwankwaso, ya roki 'yan siyasa su maida hankali wajen gina mutane maimakon wawure kuɗin gwamnati.

Tsohon gwamnan Kano ya baiwa yan siyasa wannan shawarin ne a Minna, babban birnin jihar Neja ranar Alhamis a wurin taron lakcar zababben gwamna, Muhammad Bago.

Kwankwaso.
Kwankwaso Ga Yan Siyasa: Ku Daina Satar Kuɗin Talakawa, Ku Rika Gina Al'umma Hoto: Rabiu Kwankwaso.
Asali: Facebook

A kalamansa ya ce:

"Kuɗi ba su ne komai ba, ya kamata 'yan siyasa su ɗauri niyyar bunkasa rayuwar mabuƙata da talakawa."

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan ka zabi siyar da gidaje da gine-ginen gwamnati, siyar da Coci ko Masallaci ga abokai da iyalanka, bayan ka sauka a mulki zaka yi nadama."

Kwankwaso ya baiwa zababben gwamnan APC shawara

Tsohon gwamna a jihar Kano ya roki zababben gwamnan jihar Neja, Muhammad Bago, ya zuba hannun jari mara adadi a ɓangaren ilimi da tsaro domin inganta jihar ko kuma nan gaba ya yi nadama.

Kwankwaso ya ƙara da cewa zuba hannun jari a ɓangaren ilimi ba zai ba da sakamako cikin ƙanƙanin lokaci ba, amma a kwana a tashi zai haifar da ɗa mai ido.

A cewar Kwankwaso, idan har gwamna mai jiran gado, Mista Bago, yana son samun nasara a mulkinsa, ya zama wajibi ya miƙe tsaye da zaran ya karbi mulki da nufin kawo ci gaba a Neja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Rusa Majalisar Kwamishinoninsa, Ya Sallami Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa

Ya bayyana cewa rashin gogewa da ilimi ne yasa gwamnoni da dama suka gaza katabus a jihohinsu bayan kwashe shekaru huɗu ko takwas a kan madafun iko.

Ina nan daram a PDP - Ortom

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Ortom Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya musanta yuwuwar cewa wata rana zai tattara kayansa ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Ortom ya sha alwashin goyon bayan shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu , domin bunƙasa tsarin Demokuradiyyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel