Kotun Koli Ta Yi Watsi da Karar Da PDP Ta Nemi a Soke Tikitin Tinubu da Shettima
- Kotun koli ta kori karar da jam'iyyar PDP ta shigar ta neman soke tikitin takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima na jam'iyyar APC
- PDP ta ɗaukaka kara zuwa Kotun koli bisa zargin cewa Shettima ya tsaya takara biyu a 2023 kuma ya saɓa wa dokar zaɓe
- Sai dai Alkalan Kotu lamba ɗaya a Najeriya sun yi watsi da karar saboda PDP ba ta da hurumi shiga harkokin APC
Abuja - Kotun ƙoli a Najeriya ta yi watsi da ƙarar da aka shigar gabanta, wacce ta ɓukaci ta soke halascin takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki na APC.
Kwamitin alkalai 5 na Kotun daga ke sai Allah ya isa ne suka yanke wannan hukuncin ranar Jumu'a 26 ga watan Mayu, 2023 kan ƙarar wacce jam'iyyar PDP ta shigar.
Kwamitin Alkalan ya bayyana cewa PDP ba ta hurumin shigar da wannan ƙara kasancewar ba mambar jam'iyyar APC bace, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Jam'iyyar PDP ta hannun lauyanta, Mike Ozekhome (SAN), ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ƙoli bisa zargin Shettima ya tsaya takara biyu a babban zaben 2023 da ya gabata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar lauyan PDP, Shettima ya nemi takarar Sanatan Borno da tsakiya da kuma mataimakin shugaban ƙasa, kuma hakan ya saɓa wa tanadin sashi na 29(1), 33, 35, da 84(1)(2) a kundin dokokin zaɓe 2023.
Amma da take yanke hukunci, Kotun ƙoli ta ce PDP ba ta da hurumin shigar da ƙara kan lamarin sabida ba mambar APC bace, bisa haka ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya.
Yadda shari'ar ta faro tun daga babbar Kotun tarayya
Tun da farko, Babbar Kotun tarayya da kuma Kotun ɗaukaka kara duk sun kori karar bisa hujjar rashin hurumin PDP kuma sun ci tarar babbar jam'iyyar adawa kuɗi miliyan N5m.
Daily Trust ta tattaro cewa a ranar 13 ga watan Janairu, mai shari'a Inyang Ekwo na babbar Kotun tarayya ya yi watsi da ƙarar ta PDP.
Jirgin saman Najeriya na dab da isowa Abuja
A wani labarin kuma Jirgin Saman Najeriya Ya Shirya Kamo Hanya Zuwa Birnin Tarayya Abuja, Mun Ɗauko Bidiyo.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawarin cewa jirgin 'Nigeria Air' zai fara aiki ba kama hannun yaro kafin wa'adin mulkinta ya ƙare a watan Mayu.
Asali: Legit.ng