Kotun Zabe Ta Yi Fatali da Karar Jam'iyyu 2 da Suka Kalubalanci Nasarar APC

Kotun Zabe Ta Yi Fatali da Karar Jam'iyyu 2 da Suka Kalubalanci Nasarar APC

  • Kotun sauraron karar zaben gwamnan Legas ta kori karar da jam'iyyun APM da APC suka kalubalanci nasarar APC a 2023
  • Alkalin Kotun, mai shari'a Arum Ashom ne ya yanke wannan hukunci ranar Laraba bayan jam'iyyun sun janye ƙarar
  • Wannan na zuwa ne kwanaki 5 gabanin ranar da za'a rantsar da gwamna Sanwo-Olu karo na biyu a kan mulki

Lagos - Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan jihar Legas, ranar Laraba, 24 ga watan watan Mayu, ta kori ƙarar da Allied Peoples’ Movement (APM) da Action Peoples Party (APP).

Jam'iyyun biyu sun kalubalanci nasarar da gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, suka samu a zaben gwamnan da ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamna Sanwo-Olu.
Kotun Zabe Ta Yi Fatali da Karar Jam'iyyu 2 da Suka Kalubalanci Nasarar APC Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Facebook

A rahoton Punch, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da jam'iyyar APC na cikin waɗanda ake tuhuma a ƙarar da jam'iyyun suka shigar gaban Kotun zaɓen.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Baiwa Peter Obi Wa'adin Da Zai Gabatar da Shaidu Kan Nasarar Tinubu

Yadda Kotun zabe ta yi watsi da karar jam'iyyun

Shugaban kwamitin alƙalan kotun, mai shari'a Arum Ashom, ne ya yi fatali da kararrakin bayan masu ƙarar sun sanar da janyewa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyun APM da APP ta bakin lauyoyinsu, Henry Bello da Francis Ese, sun faɗa wa Kotun zabe cewa waɗanda suke wa aiki ba su sha'awar ci gaba da ja'inja kan batun.

Tun da farko, masu ƙarar sun yi ikirarin cewa zababben gwamna, Babajide Sanwo-Olu, da mataimakinsa ba su cancanci shiga babban zaben 2023 da aka kammala ba.

Haka nan sun kuma yi musun cewa hukumar zaɓe INEC ta gaza biyayya ga dokokin zaɓe da kuma kundin mulkin Najeriya 1999 wanda aka yi wa garambawul.

Kotu ta yanke hukunci

Bayan sauraron lauyoyin APM da APP waɗanda suka sanar da janye ƙara, Alkalin ya yanke hukuncin korar ƙararrakin baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar Labour Ta Dauki Matakin Hambarar Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Gwamnan Abia

Gwamnan Legas ya ɗauki mataki gabanin ranar rantsarwa

A wani rahoton kuma Gwamnan Legas Ya Umarci Kwamishinoni Su Faɗi Abinda Suka Tara Na Sukiya, Sannan Su Sauka Daga Mukamansu Ya Sallame Su.

Babajide Sanwo-Olu ya rushe majalisar zartarwa tare da koran dukkan hadimansa daga aiki a shirye-shiryen rantsuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel