Jirgin Saman Najeriya Ya Shirya Tsaf Zai Kamo Hanya Zuwa Abuja

Jirgin Saman Najeriya Ya Shirya Tsaf Zai Kamo Hanya Zuwa Abuja

  • Jirgin saman Najeriya ya shirya tsaf zai kamo hanyar zuwa birnin tarayya Abuja kwanaki 3 gabanin miƙa mulki
  • Gwamnatin Buhari ta jima da ɗaukar alkawarin cewa kafin Buhari ya sauka, jirgin zai fara aiki a Najeriya
  • Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce jirgin zai iso gida Najeriya ranar Jumu'a 26 ga watan Mayu, 2023

Jirgin saman Najeriya (Nigerian Air) ya shirya tsaf zai taso zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa a halin yanzu jirgin yana birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia, yana ƙarisa shirye-shiryen kamo hanya zuwa babban birnin Najeriya.

Jirgin saman Najeriya.
Jirgin Saman Najeriya Ya Shirya Tsaf Zai Kamo Hanya Zuwa Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki alkawarin cewa jirgin zai fara aiki kafin karewar wa'adin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mulki Ya Kare, An Tona Asirin Masu Janyewa Daga Jikin Buhari Su Koma Tinubu

Sai dai har kawo yau, kwanaki ƙalilan gabanin shugaba Buhari ya miƙa mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wannan alƙawari bai cika ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da yake martani kan cece-kucen da ake kan batun, Ministan sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika, ya jaddada cewa jirgin zai fara jigila gabanin Buhari ya sauka.

Da yake jawabi ga Channels Tv a wata hira, Sirika ya ce:

"Game da tambayar da kuka mun kan Nigeria Air, ranar Jumu'a nan da kwana biyu kenan, Jirgin saman Najeriya zai iso Najeriya a wani ɓangaren shirin fara aiki."
"A wannan rana zamu kaddamar da jirgin, komai na jikinsa zai kasance da kalolin Najeriya kuma mallakin kamfanin Nigeria Air, daga nan zai wuce a masa sabis."

A cewar wata majiya jirgin na ɗauke da fentin kalolin Najeriya kuma shirye-shirye sun yi nisa na kamo hanya zuwa Abuja daga Ethiopia daidai lokacin da Sirika ya yi waɗannan kalamai.

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Amma babu tabbacin Jirgin zai cika sharuɗɗan fara aiki a ɗan kankanin lokacin duk da abubuwan da ke faruwa a hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasa (NCAA).

Bidiyon jirgin gabanin tasowa zuwa Abuja

Makusantan Buhari Sun Fara Janye Wa Suna Komawa Wurin Tinubu

A wani rahoton na daban kuma Yayin da mulki ya zo karshe, hadiman Buhari da ke sulalewa suna komawa wurin Tinubu sun bayyana.

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaba Muhammadu Buhari, ya ce wannan ba sabon abu bane domin ɗabi'a ce ta ɗan adam ya sauya wuri don cimma burinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel