Na Yafe Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Ortom

Na Yafe Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Ortom

  • Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa ya yafe wa shugaba Muhammadu Buhari dukkan laifin da ya masa
  • Ortom, mamban jam'iyyar PDP ya sha takun saƙa da musayar yawu da fadar shugaban ƙasa kan matsalar tsaron jihar Benuwai
  • Ya ce a matsayinsa na mabiyin Addinin kirista, ya hakura da komai, ya kuma shawarci shugaban ƙasa kan shirinsa na komawa Nijar

Benue - Gwamnan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya, Samuel Ortom, ya ce shi a karan kansa ya yafe wa shugaba Muhammadu Buhari kura-kuran da ya masa.

Gwamna Ortom ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin 'Morning show' na kafar watsa labarai Arise TV ranar Laraba 24 ga watan Mayu, 2023.

Ortom da Buhari.
Na Yafe Wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Ortom Hoto: Samuel Ortom, Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ortom, mamban tawagar G-5 a jam'iyyar PDP, ya soki fadar shugaban ƙasa bisa ɗora laifin kashe-kashen da ke aukuwa a jihar Benuwai kan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Jamhuriyar Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Bayan Na Sauka Daga Mulki, Buhari

Ya ayyana kokarin shugaba Muhammadu Buhari na ɗora wannan ɗanyen aiki kan gwamnatinsa da, "Makircin juya yanayi da tarihin abinda ya auku."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Punch ta tattaro cewa a kwanakin baya, shugaba Buhari ya roƙi 'yan Najeriya waɗanda mai yuwuwa ya ɓata musu rai a lokacin mulkinsa, su yi haƙuri su yafe masa.

Abinda ya sa na yafe wa Buhari - Ortom

Gwamna Ortom, wanda ya kafa hujja da Littafin addinin Kirista Bible, ya ƙara da cewa ya yafe wa shugaban ƙasa, wanda zai sauka nan da kwanaki 5 masu zuwa.

A kalamansa ya ce:

"Idan baku haƙura kun yafe ba, Allah ba zai yafe muku ba. Ni a matsayina na ɗalibi mai koyon Bible kuma haifaffe a addinin Kirista, na yafe wa shugaban ƙasa Buhari."
Ortom ya bayyana fatan sabuwar gwamnatin zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zata yi kokari fiye da yanzu a jihar Benuwai da ma ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

"Muna fatan gwamnati mai kamawa karkashin Bola Tinubu zata samar da tallafi, taimako, tsaro, habaka tattalin arziƙi da kuma zaman lafiya ga al'umma. Mun sha wahala tsawon shekaru 8."

Ortom ya aike da saƙo ga Buhari

Bayan haka, Gwamna Ortom ya shawarci Buhari kar ya ɗauki matakin barin Najeriya, ya tsaya ya haɗa hannu da gwamnatin Tinubu domin ceto ƙasar nan.

"Babu buƙatar ya koma Nijar da zama, ya zauna a gida Najeriya tare da mu. Ya kamata baki ɗayanmu mu taimakawa gwamnati.mai zuwa kuma izinin Allah zamu taso daga ƙasa zuwa sama."

Gwamnan Legas ya rushe majalisar zartarwa

A wani labarin kuma Gwamnan Legas Ya Umarci Kwamishinoni Su Faɗi Abinda Suka Tara Kan Su Sauka.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya umarci baki daya mutanrn da ya naɗa a muƙamai su fara shirin miƙa mulki kuma su bayyana wa duniya dukiyar da suka mallaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel