Ya Kamata Shugaban Majalisar Dattawa Ya Kasance Kirista Saboda Hadin Kan Najeriya - Shettima

Ya Kamata Shugaban Majalisar Dattawa Ya Kasance Kirista Saboda Hadin Kan Najeriya - Shettima

  • Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Kashim Shettima ya magantu kan wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba
  • Shettima ya ce Sanata Godswill Akpabio ya cancanci darewa kan kujara ta uku a kasar domin yin adalci da daidaito
  • Ya ce kirista ne ya kamata ya hau matsayin duba ga cewar zababben shugaban kasar da mataimakinsa duk musulmai ne

Abuja - Zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce shugabancin APC da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun zabi Godswill Akpabio don ya zama shugaban majalisar dattawa ta 10 ne domin daidaita harkokin siyasa.

Shettima ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi ga zababbun sanatoci, wadanda suka kasance mambobin kungiyar da ke goyon bayan Akpabio da Barau a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa a ofishin kamfen dinsa da ke Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima
Ya Kamata Shugaban Majalisar Dattawa Ya Kasance Kirista Saboda Hadin Kan Najeriya - Shettima Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Ya ce:

"Zababben shugaban kasar da zababben mataimakin shugaban kasa duk Musulmai ne. Don ra'ayin zaman lafiya da hadin kan kasar nan ne cewa ya kamata a mika kujera ta gaba ga kirista, idan ba haka ba, zai ci gaba da tabbatar da zargin da ake na cewa gwamnatin APC na da ajandar Musuluntar da kasar. Za a dauki hakan a matsayin cin mutuncin yan uwanmu Kiristoci wadanda suka tsaya ka'in da na'in don mara mana baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan ne dalilin da yasa na ji dadin zabin shugabancin jam'iyyar cewa ya kamata dan uwana kuma jagora Sanata Godswill Akpabio ya zama mutum na uku a kasar nan. Daidaituwar kasar nan ya fi muhimmanci bisa ga duk wani ra'ayi na siyasa da za mu yi tunani a kai. Muna bukatar samun kasa mai hadin kai kafin mu yi maganar siyasa da mukamai."

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Akpabio ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa, Shettima

Shettima ya ce Akpabio yana da wayewa, cancanta da gogewar da ake bukata don hawa kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10, haka Sanata Barau, mataimakinsa.

Ya ce:

"Baya ga bukatar daidaita lamarin addini, cancanta da gogewa ma sun taka rawar gani a zabinmu."

Shettima ya yi alkawarin tuntubar zababbun sanatocin APC da basu riga sun ba da kai bori ya hau ba kan zabin jam'iyyar, rahoton Nigerian Tribune.

An yi cacar baki tsakanin Gbajabiamila da Wase a zauren majalisa

A wani labari na daban, mun ji cewa cacar baki ta kaure tsakanin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakinsa, Idris Wase.

Gabajabiamila ya bayar da wata sanarwa inda ya bukaci a takaita takardar oda na ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu saboda su samu damar halartan bikin kaddamar da hedkwatar NILDS da za a yi wanda shi kuma Wase ya nuna adawa ga hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel