Gwamna Makinde Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Kori Hadimansa

Gwamna Makinde Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Kori Hadimansa

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya rushe majalisar zartarwa, ya sallami hadiman da ya naɗa a gwamnatinsa
  • Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya futar ranar Talata
  • Ya ce gwamna ya umarci su miƙa duk wata kadarar gwamnati hannun babban ma'aikacin da ke wurin da suka jagoranta

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na jam'iyyar PDP ya sanar da rushe majalisar zartarwa ta gwamnatinsa ranar Talata 23 ga watan Mayu, 2023.

Bayan haka Makinde ya soke dukkan naɗe-naɗen siyasa da ya yi a zangon mulkinsa na farko, inda ya roki masu riƙe da muƙaman su miƙa kayan gwamnati da ke hannunsu.

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamna Makinde Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Kori Hadimansa Hoto: Seyi Makinde/Facebook
Asali: Facebook

Yaushe matakin zai fara aiki?

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan matakin da gwamnan ya ɗauka zai fara aiki ne nan take daga lokacin da saƙo ya isa ga kowane mai riƙe da muƙami.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai matakin bai shafi masu rike da muƙaman hukumomin da doka ta tanadar musu wa'adi ba.

Makinde ya sanar da haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 23 ga watan Mayu ɗauke da a hannun shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Oyo kuma shugaban kwamitin miƙa mulki, Otunba Segun Ogunwuyi.

Punch ta rahoto a Sanarwan, Mista Ogunwuyi ya ce:

"Mai girma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya umarce ni na faɗa muku cewa ya rushe majalisar zartaswan jiha kuma ya sallami dukkan hadiman da ya naɗa daga yau Talata, 23 ga watan Mayu, 2023."
"Ana umartan dukkan masu rike da muƙamai (kama daga kwamishinoni, hadimai da shugabannin hukumomi) su miƙa kayayyakin gwamnati ga manyan ma'aikatan da ke wurin da suka yi aiki."
"Haka na masu rike da muƙamai a hukumomi waɗanda doka ta tanadi wa'adin da zasu shafe kan kujerunsu, wannan umarnin bai shafe su ba."

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Bugu da ƙari, gwamna Makinde ya yaba musu bisa ɗumbin gudummuwar da suka bayar wajen kawo ci gaba a jihar Oyo kana ya musu fatan Alheri a duk abinda suka a gaba.

Ganduje ya fara shirin sauka daga mulkin Kano

A wani labarin kuma Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartaswa Mako Ɗaya Gabanin Mika Mulki.

Gwamnan ya umarci dukkan waɗanda matakin ya shafa su mika ragamar ma'aikatunsu hannun manyan Sakatarori da daraktoci daga nan zuwa ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel